YouVersion Logo
Search Icon

Zab 102

102
Addu'ar Wanda Yake Shan Wahala
1Ka ji addu'ata, ya Ubangiji,
Ka ji kukana na neman taimako!
2Kada ka ɓoye mini sa'ad da nake shan wahala!
Ka ji ni, ka amsa mini da sauri sa'ad da na yi kira!
3Raina ya ɓace kamar hayaƙi,
Jikina yana ƙuna kamar wuta.
4An tattake ni kamar busasshiyar ciyarwa,
Ba ni da marmarin cin abinci.
5Ina nishi da ƙarfi,
Ba abin da ya ragu gare ni,
In banda ƙashi da fata.
6Ni kamar tsuntsu nake cikin hamada,
Kamar mujiya a kufai.
7Kwana nake ba barci,
Na zama kamar tsuntsun da yake fama da kewa
A bisa kan ɗaki.
8Maƙiyana suna cin mutuncina dukan yini.
Waɗanda suke mini ba'a,
Suna la'antarwa da sunana.
9Toka ce abincina,
Hawayena kuwa sun gauraya da abin shana,
10Sabili da fushinka da hasalarka.
Ka ɗauke ni, ka jefar da ni.
11Raina kamar inuwar maraice yake,
Kamar busasshiyar ciyawa nake.
12Amma kai, ya Ubangiji, sarki ne kai har abada,
Dukan zamanai masu zuwa za su tuna da kai.
13Za ka tashi ka ji tausayin Sihiyona,
Lokaci ya yi da za ka yi mata jinƙai,
Wannan shi ne lokacin!
14Bayinka suna ƙaunarta,
Ko da yake an hallakar da ita,
Suna jin tausayinta,
Ko da yake ta zama kufai.
15Sauran al'umma za su ji tsoron Ubangiji,
Dukan sarakunan duniya za su ji tsoron ikonsa.
16Sa'ad da Ubangiji ya sāke gina Sihiyona
Zai bayyana girmansa.
17Zai saurari jama'arsa wadda ya rabu da ita,
Zai kuwa ji addu'arta.
18Ku rubuta abin da Ubangiji ya aikata don zamani mai zuwa,
Don waɗanda ba a haife su ba tukuna,
Su ma su yabe shi.
19Ubangiji ya duba ƙasa
Daga Sama, tsattsarkan wurinsa,
Daga Sama ya dubi duniya,
20Don ya ji nishin ɗaurarru,
Don ya saki waɗanda aka yanke musu hukuncin kisa.
21Saboda wannan mutane za su yi shelar sunan Ubangiji a Sihiyona,
Za su yi masa godiya a Urushalima,
22Sa'ad da sauran al'umma da mulkoki suka taru
Don su yi wa Ubangiji sujada.
23Tun ina ƙaramin yaro Ubangiji ya sa na rasa ƙarfi,
Ya gajerta kwanakina.
24Ya Allahna, kada ka ɗauke ni a yanzu,
Tun da yake ban tsufa ba tukuna!
Ya Ubangiji har abada kake.
25 # Ibr 1.10-12 Ka halicci duniya tun tuntuni,
Da ikonka ne ka yi sammai.
26Su za su ɓace duka, amma kai za ka dawwama,
Za su ƙare kamar yadda tufafi suke ƙarewa,
Za ka sāke su kamar tufafi, za su kuwa ɓace.
27Amma kai, kana yadda kake kullayaumin,
Har abada kake.
28'Ya'yanmu za su yi zaman lafiya,
Zuriyarsu kuma za su zauna cikin kiyayewarka kullayaumin.

Currently Selected:

Zab 102: HAU

Highlight

Share

Compare

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in

Video for Zab 102