K.Mag 30
30
Hikimar Agur
1Waɗannan su ne maganar Agur ɗan Yake, da ya yi wa Etiyel da Yukal,
2“Hakika wautata ta sa na zama kamar dabba ba mutum ba,
Ba ni kuwa da fahimi irin na mutum.
3Ban koyi hikima ba,
Ban kuwa san kome game da Allah ba.
4Wa ya taɓa hawa cikin Sama ya sauko?
Wa ya taɓa kama iska cikin tafin hannunsa?
Wa ya taɓa ƙunshe ruwa cikin rigarsa?
Wa kuma ya kafa iyakar duniya?
Ina sunansa, ina kuma sunan ɗansa?
Hakika ka sani!
5“Kowace maganar Allah takan tabbata. Shi garkuwa ne ga waɗanda suke fakewa a wurinsa. 6Kada ka yi ƙari a kan maganarsa, don kada ya tsauta maka, a kuma bayyana kai maƙaryaci ne.”
Waɗansu Karin Magana kuma
7Abu biyu na roƙe ka, kada ka hana mini su kafin in mutu. 8Ka kawar da ƙarya nesa da ni. Kada ka ba ni talauci ko dukiya, sai dai ka ba ni abinci daidai da bukatata, 9don kada in wadata, har in yi musunka, in ce, “Wane ne Ubangiji?” Kada kuwa in yi talauci har in yi sata in saɓi sunan Allahna.
10Kada ka kushe bara a wurin maigidansa domin kada ka yi laifin da zai sa a la'ance ka.
11Akwai waɗansu mutane da sukan zagi iyayensu maza, ba sukan kuma nuna godiya ga iyayensu mata ba.
12Akwai waɗansu mutanen da suke ganin kansu tsarkaka ne, alhali kuwa ƙazamai ne su.
13Akwai waɗansu mutane da suke yi wa jama'a ƙallon raini suna ɗaurin gira.
14Akwai waɗansu mutane waɗanda haƙoransu takuba ne, mataunansu kuma wuƙaƙe ne, don su cinye matalauta da masu fatara daga duniya.
15-16Matsattsaku tana da 'ya'ya mata biyu, ana kiransu, “Ba ni, Ba ni.”
Akwai abu uku da ba su ƙoshi, i, har huɗu ma da ba su cewa, “Ya isa,” wato,
lahira,
macen da ba ta haihuwa,
ƙasa wadda ba ta ƙoshi da ruwa,
wuta wadda ba ta cewa, “Ya isa.”
17Idan ɗa ya raina mahaifi, ya kuma yi wa mahaifiya ba'a hankakin kwari za su ƙwaƙule masa idanu, 'ya'yan mikiya za su cinye.
18-19Akwai abu uku, i, har huɗu ma, waɗanda ban iya fahimtar su ba, wato,
yadda gaggafa take tashi a sararin sama,
yadda maciji yake jan ciki a kan dutse,
yadda jirgin ruwa yake tafiya a teku,
Sha'anin namiji da 'ya mace.
20Ga yadda al'amarin mazinaciya yake, takan yi sha'aninta sa'an nan ta yi wanka ta ce, “Ban yi laifin kome ba!”
21-23Akwai abu uku, i, har huɗu ma waɗanda duniya ba ta jurewa da su, wato,
bara da ya zama sarki,
wawa da ya ƙoshi da abinci,
mummunar mace da ta sami miji,
baiwar da ta gāji uwargijiyarta.
24-28Akwai ƙananan abubuwa huɗu a duniya, amma suna da hikima ƙwarai, wato,
tururuwa talikai ne marasa ƙarfi, amma duk da haka sukan tanadi abincinsu da rani,
remaye ba ƙarfafa ba ne, duk da haka suna yi wa kansu gidaje a cikin duwatsu,
fara ba su da sarki, amma duk da haka suna tafiya sahu-sahu.
ƙadangare ma wanda ka iya kama shi a hannu, amma yana zama a cikin fādodin sarakuna.
29-31Akwai abu uku, i, har huɗu ma da suke da kwarjini da taƙama a tafiyarsu, wato
Zaki wanda ya fi dukan dabbobi ƙarfi, ba ya ratse wa kowa daga cikinsu,
bunsuru da zakara mai taƙama,
sarkin da yake tafiya gaban jama'arsa.
32Idan ka yi wauta kana ta ɗaukaka kanka, ko kuwa kana shirya mugunta, ka tsaya ka yi tunani! 33Gama kaɗa madara takan kawo mai, murɗa hanci takan sa a yi haɓo, tsokanar fushi takan kawo jayayya.
Currently Selected:
K.Mag 30: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979