YouVersion Logo
Search Icon

K.Mag 29

29
1Wanda ake ta tsauta wa a kai a kai, amma ya taurare, ba makawa tasa ta ƙare farat ɗaya.
2Sa'ad da masu adalci suke mulki, jama'a sukan yi murna, amma sa'ad da mugaye suke mulki, jama'a sukan yi nishi.
3Wanda yake ƙaunar hikima yana faranta zuciyar mahaifinsa.
Amma wanda yake abuta da karuwai zai lalatar da dukiyarsa.
4Sarkin da yake aikata adalci ƙasarsa za ta yi ƙarƙo, amma wanda yake karɓar rashawa zai lalatar da ƙasar.
5Mutum wanda yake yi wa maƙwabcinsa daɗin baƙi yana kafa wa kansa tarko.
6Laifin mugun zai zama tarko a gare shi, amma adali zai raira waƙa, ya yi farin ciki.
7Adali yana sane da hakkin matalauta, amma mugun bai san wannan ba.
8Ashararai sukan sa wa birni wuta, amma masu hikima sukan kwantar da hasala.
9Idan gardama ta shiga tsakanin mai hikima da wawa, sai wawa ya yi ta fushi, ko kuwa ya yi ta dariya, gardamar dai ba za ta ƙare ba.
10Mutane masu kisankai suna ƙin amintaccen mutum, amma adalai za su kiyaye ransa.
11Wawa yakan nuna fushinsa ko yaushe, amma mutum mai hikima yakan kanne fushinsa.
12Idan mai mulki yana kasa kunne ga maganganun ƙarya, dukan ma'aikatansa za su zama maƙaryata.
13Matalauci da azzalumi suna tarayya a abu ɗaya, wato dukansu Ubangiji ne yake ba su ganin gari.
14Idan sarki yana yi wa talakawa shari'ar gaskiya, zai daɗe yana mulki.
15Horo da tsautawa suna ba da hikima, amma yaron da aka sangarta zai jawo wa mahaifiyarsa kunya.
16Sa'ad da mugaye suke mulki, laifofi suka ƙaru, amma adalai za su ga faɗuwar waɗannan mutane.
17Ka hori ɗanka zai daɗaɗa maka rai, ya kuma faranta maka zuciya.
18Inda ba a bin faɗar Allah, jama'a za su kangare, amma mai farin ciki ne wanda yake kiyaye dokar Allah.
19Bara ba ya horuwa ta wurin magana kawai, gama ko da ya fahimta ma, ba zai kula ba.
20Ka ga mutum mai garajen yin magana? To, gara a sa zuciya ga wawa da a sa zuciya gare shi.
21Baran da aka shagwaɓa tun yana yaro, a ƙarshe zai ɗauki kansa tankar magājin gida.
22Mutum mai saurin fushi yakan ta da faɗa, mai zafin rai kuma yakan aikata laifi da yawa.
23Girmankan mutum zai jawo masa ƙasƙanci, amma za a girmama mai tawali'u.
24Abokin ɓarawo mugun maƙiyin kansa ne, yana jinsa yana ta rantsuwa, amma ba zai ce kome ba.
25Jin tsoron mutane tarko ne, amma wanda ya dogara ga Ubangiji za a ɗaukaka shi.
26Mutane da yawa sukan nemi farin jini daga wurin mai mulki, amma Ubangiji ne yake yi wa mutum adalci.
27Mutum marar gaskiya abin ƙyama ne ga adali, adali kuma abin ƙyama ne ga mugun.

Currently Selected:

K.Mag 29: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in