YouVersion Logo
Search Icon

K.Mag 31

31
Shawara ga Sarki
1Wannan ita ce maganar sarki Lamuwel wadda uwarsa ta koya masa.
2“Mene ne, ɗana? Mene ne, ya ɗana ne cikina? Mene ne, ɗana na wa'adi? 3Kada ka ba da ƙarfinka ga mata, kada kuwa ka mai da hankali gare su, waɗanda suke hallaka sarakuna. 4Bai dace ba, ya Lamuwel, bai dace ba ko kaɗan, sarakuna su sha ruwan inabi, ko masu mulki su yi marmarin barasa, 5don kada su sha su manta da doka, su kuma kauce wa gaskiya a shari'ar waɗanda aka zalunta. 6A ba da barasa ga wanda yake cikin halin ƙaƙa naka yi, ruwan inabi kuma ga waɗanda suke cikin ɓacin rai. 7Bari ya sha don ya manta da talaucinsa, don kada kuma ya ƙara tunawa da ɓacin ransa.
8“Ka yi magana domin bebaye, domin kuma hakkin dukan waɗanda ba su da wani mataimaki.(1Sam 19.4; Ayu 29.12-17) 9Ka yi magana dominsu, ka yi shari'ar adalci, ka kiyaye hakkin matalauta da masu bukata.”
Yabon Macen Kirki
10Wa yake iya samun cikakkiyar mace? Darajarta ta fi ta lu'ulu'ai.
11Mijinta yakan amince da ita, ba kuwa zai yi hasara ba.
12Takan yi masa alheri ba mugunta ba, dukan kwanakinta.
13Takan samo ulu da lilin, ta yi saƙa da hannuwanta da farin ciki.
14Takan kawo abincinta daga nesa, kamar fatake.
15Takan yi asubanci ta shirya wa iyalinta abinci, ta kuma shirya wa 'yan matan gidanta aike-aiken da za su yi.
16Takan lura da gona sosai kafin ta saya, da ribar da ta ci take dasa gonar inabi.
17Takan himmantu ta yi aiki tuƙuru.
18Ta sani akwai riba a cikin kasuwancinta. Fitilarta na ci dare farai.
19Da hannunta take kaɗi, tana kuma saƙa da hannuwanta.
20Takan yi wa matalauta da masu fatara karamci.
21Ba ta jin tsoron lokacin sanyi gama 'ya'yanta duka suna da tufafi masu ƙauri.
22Takan yi wa gadonta kayan shimfiɗa, tufafinta kuma na lilin ne mai laushi na shunayya.
23Mijinta sananne ne a dandali, sa'ad da yake zaune tare da dattawan gari.
24Takan yi riguna na lilin ta sayar, takan kuma sayar wa fatake da abin ɗamara.
25Wadata da mutunci su ne suturarta. Ba ta jin tsoron tsufa.
26Tana magana da hikima. Koyarwarta ta alheri ce.
27Tana lura da al'amuran 'ya'yanta da kyau. Ba ruwanta da ƙyuya.
28'Ya'yanta sukan tashi su gode mata, mijinta kuma yana yabonta.
29Ya ce, “Mata da yawa sun yi abin yabo, amma ke kin fi su duka.”
30Kayan tsari da jamali duk banza ne, amma mace mai tsoron Ubangiji, ita ce abar yabo.
31A yi mata cikakken yabo saboda ayyukanta, za a yabi ayyukanta a dandali.

Currently Selected:

K.Mag 31: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in