K.Mag 14
14
1Hikimar mata takan gina gidaje, amma wauta takan rushe su.
2Ka yi gaskiya, za ka nuna girmamawarka ga Ubangiji, amma idan ka yi rashin gaskiya, ka nuna rashin girmamawa ke nan ga Ubangiji.
3Kalmomin mai hikima za su kiyaye shi, amma maganganun wawa za su jawo masa hukunci.
4Idan ba ka da shanun noma ba za ka sami hatsi mai yawa ba, amma idan kana da su za ka sami hatsi mai yawan gaske.
5Amintaccen mashaidi a ko yaushe yana faɗar gaskiya, amma marar aminci ba ya faɗar kome, sai ƙarairayi.
6Mutum mai fāriya ba zai taɓa zama mai hikima ba sam, amma mutum mai basira yakan koya a sawwaƙe.
7Ka nisanci wawaye, gama ba su da abin da za su koya maka.
8Me ya sa haziƙi yake da hikima? Domin ya san abin da zai yi. Me ya sa dakiki yake wauta? Domin yana ganin kansa masani ne.
9Idan wawaye sun yi zunubi ba sukan kula ba, amma mutanen kirki sukan nemi gafara.
10Ɓacin ranka naka ne, murnarka kuwa ba za ka raba da wani ba.
11Gidan mutumin kirki ba zai rushe ba bayan da an lalatar da gidan mugun mutum.
12 #
K.Mag 16.25
Hanyar da kake tsammani ita ce daidai, za ta kai ka ga hallaka.
13Dariyar mutum takan ɓoye baƙin cikinsa. Sa'ad da murna ta tafi, ko yaushe baƙin ciki yana nan.
14Mugu zai sami abin da ya cancance shi, mutumin kirki kuma zai sami sakayyar ayyukansa.
15Wawa yakan gaskata kowane abu, amma mai la'akari yana lura da takawarsa.
16Mutum mai hankali yana lura don ya kauce wa wahala, amma wawa rashin kula gare shi, yakan aikata kome da gaggawa.
17Mutum mai zafin rai yakan yi aikin wauta, mai mugayen dabaru kuma abin ƙi ne.
18Jahilai sukan sami abin da ya cancanci wautarsu, amma ilimi shi ne sakamakon masu azanci.
19Tilas mugaye su rusuna wa adalai, su roƙe su tagomashi da tawali'u.
20Ba wanda yake son matalauci, amma attajiri yana da abokai da yawa.
21Idan kana so ka zama mai farin ciki, sai ka nuna alheri ga matalauci. Zunubi ne ka raina kowane mutum.
22Waɗansu za su amince da kai, su girmama ka, idan ka aikata nagarta, idan kuwa ka aikata mugunta, to, ka yi babban kuskure.
23Idan ka yi aiki za ka sami abin masarufi, idan kuwa ka zauna kana ta surutu kawai za ka zama matalauci.
24Mutane masu hikima za a sāka musu da wadata, amma za a san wawa ta wurin wautarsa.
25Sa'ad da mashaidi ya faɗi gaskiya zai ceci rayuka, amma maƙaryacin mashaidi yakan ci amanar mutane sa'ad da ya faɗi ƙarairayi.
26Tsoron Ubangiji yakan ba da tabbatarwa, da zaman lafiya ga mutum da iyalinsa.
27Kana so ka kauce wa mutuwa? To, tsoron Ubangiji shi ne maɓuɓɓugar rai.
28Darajar sarki ta dogara ga irin yawan mutane da ya mallaka, idan ba su, shi ba kome ba ne.
29Mutum mai kamewa yana da hikima, amma mai zafin rai yana bayyana wautarsa a fili.
30Kwanciyar rai lafiya ce ga jiki, amma kishi yana kama da ciwon da yake cin ƙashi.
31Wanda ya zalunci matalauci ya zargi Mahaliccinsa ke nan, amma nuna alheri ga matalauci yin sujada ne.
32Muguntar mugun takan kawo hallakarsa, amma adalin mutum, an kiyaye shi ta wurin dattakonsa.
33Hikima tana cikin kowane tunani na haziƙi, wawa bai san kome game da hikima ba.
34Adalci yakan ɗaukaka al'umma, amma zunubi yakan kunyatar da al'umma.
35Sarakuna suna jin daɗin ƙwararrun 'yan majalisarsu, amma sukan hukunta waɗanda suka ba su kunya.
Currently Selected:
K.Mag 14: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979