K.Mag 15
15
1Amsa magana da tattausan harshe takan kwantar da hasala, amma magana da kakkausan harshe takan kuta fushi.
2Sa'ad da mai hikima ya yi magana yakan sa ilimi ya yi bansha'awa, amma wawaye sukan yi ta sheƙa rashin hankali.
3Ubangiji yana ganin abin da yake faruwa a ko'ina, yana lura da mu, ko muna aikata alheri ko mugunta.
4Kalmomin alheri suna kawo rai, amma maganganun ƙiyayya suna karya zuciyar mutum.
5Wauta ce mutum ya ƙi kulawa da abin da mahaifinsa ya koya masa, amma hikima ce idan ka karɓi tsautawarsa.
6Adalai suna adana dukiyarsu, amma mugaye sukan rasa tasu dukiya sa'ad da wahala ta zo.
7Mutane masu hikima suke yaɗa ilimi, amma banda wawaye.
8Ubangiji yana murna sa'ad da adalai suke yin addu'a, amma yana ƙin hadayun da mugaye suke miƙa masa.
9Ubangiji yana ƙin hanyoyin mugaye, amma yana ƙaunar mutumin da yake yin abin da yake daidai.
10Idan ka yi abin da ba daidai ba, za ka sha hukunci sosai, za ka mutu idan ka ƙi yarda da tsautawa.
11Ko lahira ba za ta hana Ubangiji ya san abin da yake can ba. Ƙaƙa fa mutum zai iya ɓoye wa Allah tunaninsa?
12Mai girmankai ba ya so a tsauta masa. Faufau ba zai nemi shawara a wurin masu hikima ba.
13Sa'ad da mutum yake murna yakan yi murmushi, amma sa'ad da yake baƙin ciki yakan yi nadama.
14Mutum mai basira yana neman ilimi, amma dakikai, jahilcinsu ya wadace su.
15Wahaltaccen mutum a ko yaushe, fama yake yi a zamansa, amma masu farin ciki suna zama da daɗin rai.
16Gara a zauna da talauci da tsoron Ubangiji, da a sami dukiya game da wahala.
17Gara cin mabunƙusa tare da waɗanda kake ƙauna, da ka ci abinci mai romo a inda ƙiyayya take.
18Zafin rai yakan kawo jayayya, amma haƙuri yana kawo salama.
19Idan kai rago ne za ka gamu da wahala a ko'ina, amma idan kai amintacce ne, ba za ka sha wahala ba.
20Ɗa mai hikima yana faranta zuciyar mahaifinsa, amma wawa yana raina mahaifiyarsa.
21Dakikai suna murna da wautarsu, amma mai hikima zai aikata abin da yake daidai.
22Ka nemi dukan shawarwarin da ka iya ka samu, za ka yi nasara, idan ba tare da shawara ba, za ka fāɗi.
23Me ya fi wannan zama abin murna? Mutum ya sami maganar da take daidai a lokacin da ya dace!
24Mutum mai hikima yakan kama hanya ya haura zuwa rai, ba ya bin hanyar da ta gangara zuwa mutuwa.
25Ubangiji zai rushe gidajen masu girmankai, amma zai kiyaye dukiyar gwauruwa, wato mata wadda mijinta ya mutu.
26Ubangiji yana ƙin tunanin mugaye, amma yana murna da kalmomi masu daɗi.
27Mai ƙoƙarin cin ƙazamar riba yana jefa iyalinsa a wahala ke nan. Kada ka karɓi hanci, za ka yi tsawon rai.
28Mutanen kirki sukan yi tunani kafin su ba da amsa. Mugaye suna da saurin ba da amsa, amma takan jawo wahala.
29Sa'ad da mutanen kirki sukan yi addu'a, Ubangiji yakan kasa kunne, amma ba ya kulawa da mugaye.
30Fuska mai fara'a takan sa ka yi murna, labari mai daɗi kuma yakan sa ka ji daɗi.
31Idan ka mai da hakali sa'ad da ake tsauta maka kai mai hikima ne.
32Idan ka ƙi koyo kana cutar kanka, idan ka karɓi tsautawa za ka zama mai hikima.
33Tsoron Ubangiji koyarwa ce domin samun hikima. Sai ka zama mai tawali'u kafin ka sami girmamawa.
Currently Selected:
K.Mag 15: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979