YouVersion Logo
Search Icon

K.Mag 13

13
1Ɗa mai hikima yakan mai da hankali sa'ad da mahaifinsa yake kwaɓarsa, amma mutum mai girmankai ba ya yarda da kuskurensa.
2Mutanen kirki za a sāka musu da alheri a kan abin da suke faɗa, amma mayaudara sukan ƙosa su ta da zaune tsaye.
3Ka lura da irin abin da kake faɗa don ka kiyaye ranka. Mutumin da bai kula da maganarsa ba, yakan hallakar da kansa.
4Rago yakan ƙosa ya sami wani abu ainun, amma sam, ba zai samu ba. Mai mai da hankali ga aikinsa zai sami kowane abu da yake bukata.
5Masu aminci suna ƙin ƙarairayi, amma maganganun mugun abin kunya ne da ƙasƙanci.
6Adalci yakan kiyaye marasa laifi, amma mugunta ita ce fāɗuwar masu zunubi.
7Waɗansu mutane sukan nuna su attajirai ne, alhali kuwa ba su da kome. Waɗansu kuma sukan nuna su matalauta ne, alhali kuwa suna da dukiya.
8Kuɗin attajiri suna iya ceton ransa, bai kyautu ba a razana matalauci.
9Adalai suna kama da haske mai haskakawa ƙwarai, mugaye kuwa suna kamar fitilar da take mutuwa.
10Fāriya ba ta kawo kome sai wahala. Hikima ce a nemi shawara.
11Dukiyar da aka same ta a sawwaƙe, za ka rasa ta da sauri, amma wanda ya same ta da wahala, za ta yi ta ƙaruwa.
12Idan ba bege, sai zuciya ta karai, amma muradin da ya tabbata zai cika ka da sa zuciya.
13Idan ka ƙi shawara mai kyau wahala kake nemar wa kanka, idan ka bi ta kuwa za ka zauna lafiya.
14Koyarwar masu hikima maɓuɓɓugar rai ce, za ta taimake ka ka kuɓuta sa'ad da ranka yake cikin hatsari.
15Basira takan sa a girmama ka, amma mutanen da ba za a iya amincewa da su ba, a kan hanyar hallaka suke.
16Mutum mai hankali a ko yaushe yakan yi tunani kafin ya aikata, amma wawa yakan tallata jahilcinsa.
17Manzanni marasa aminci sukan haddasa wahala, amma waɗanda suke amintattu sukan kawo salama.
18Mutumin da ba zai koya ba, zai talauce ya sha kunya, amma wanda ya kasa kunne ga tsautawa za a girmama shi.
19Abu mai kyau ne mutum ya sami biyan bukatarsa! Wawaye sukan ƙi barin mugunta.
20Ka koya daga wurin masu hikima, za ka zama mai hikima. Yi abuta da wawaye, za ka kuwa lalace.
21Wahala tana bin masu zunubi ko'ina, amma za a sāka wa adalai da kyawawan abubuwa.
22Mutumin kirki zai sami dukiya, har ya bar wa jikokinsa, amma dukiyar masu zunubi za ta zama ta adalai.
23Saurukan da ba a aikatawa, za su ba da isasshen abinci ga matalauci, amma mutane marasa gaskiya sukan hana albarka.
24Idan ba ka horon ɗanka, ba ka ƙaunarsa ke nan, amma idan kana ƙaunarsa za ka riƙa kwaɓarsa.
25Adalai suna da isasshen abinci, amma mugaye fama suke da yunwa ko yaushe.

Currently Selected:

K.Mag 13: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in