Neh 4
4
Ma'aikata sun Tsare Kansu
1Sa'ad da Sanballat ya ji muna ginin garun, sai ya husata ƙwarai, ya yi wa Yahudawa ba'a. 2Ya yi magana a gaban 'yan'uwansa da sojojin Samariya ya ce, “Mene ne waɗannan Yahudawa kumamai suke yi? Za su mai da abubuwa yadda suka a dā ne? Za su miƙa hadayu ne? Za su gama ginin a rana ɗaya ne? Za su iya samun duwatsun gini daga tsibin matattun duwatsu?”
3Tobiya Ba'ammone yana kusa da shi, ya ce, “Ai, garun da suke ginawa da duwatsu, ko dila ya hau, sai ya rushe shi!”
4Sai ni, Nehemiya, na yi addu'a, na ce, “Ka ji, ya Allahnmu, gama ana raina mu, ka sa ba'arsu ta koma kansu, ka sa a washe su a kai su ƙasar bauta. 5Kada ka shafe laifinsu, kada kuwa ka gafarta musu, gama sun ci mutuncinmu, mu da muke gini.”
6Muka gina garun, har ya kai rabin tsayinta, domin mutane sun himmatu da aikin.
7Amma sa'ad da Sanballat, da Tobiya, da Larabawa, da Ammonawa, da mutanen Ashdod, suka ji yadda ginin garun Urushalima yake ci gaba, ana kuma tattoshe tsattsaguwa, sai suka husata. 8Dukansu suka ƙulla za su zo, su yi yaƙi da Urushalima, su ta da hankali a cikinta. 9Sai muka yi addu'a ga Allahnmu, muka sa masu tsaro su yi mana tsaro dare da rana saboda su.
10Mutanen Yahuza kuwa suka ce,
“Ƙarfin ma'aikata yana kāsawa,
Akwai komatsai da yawa da za a kwashe,
Yaya za mu iya gina garun yau?”
11Abokan gābanmu kuma suka ce, “Ba za su sani ba, ba kuwa za su gan mu ba, sai dai kawai su gan mu a cikinsu, za mu karkashe su, mu tsai da aikin.” 12Da Yahudawan da suke zaune kusa da su suka zo, suka yi ta nanata mana irin shirin abokan gabanmu, wato za su zo su fāɗa mana. 13Saboda haka na sa jama'a su ja ɗamara bisa ga iyalinsu a bayan garu, a wuraren da ba a gina ba. Suna riƙe da takuba, da māsu, da bakuna.
14Da na ga mutane sun damu, sai na tashi na yi magana da shugabanni, da sauran jama'a, na ce, “Kada ku ji tsoro, ku tuna da Ubangiji mai iko, mai banrazana, ku yi yaƙi domin 'yan'uwanku, da 'ya'yanku mata da maza, da matanku, da gidajenku.” 15Da abokan gābanmu suka ji mun san shirinsu, Ubangiji kuwa ya wargaje shirinsu, sai dukanmu muka koma wurin garun, kowa ya kama aikinsa.
16Daga wannan rana, sai rabin barorina suka yi ta gini, rabi kuwa suna riƙe da māsu, da garkuwoyi, da bakuna, da sulke. Shugabannin kuwa suka goyi bayan dukan Yahudawa sosai. 17Masu ginin garun da masu ɗaukan kaya suna yi da hannu ɗaya, hannu ɗaya kuma na riƙe da makami. 18Kowane magini yana rataye da takobinsa sa'ad da yake gini. Mai busa ƙaho yana kusa da ni. 19Sai na ce wa manya da shugabanni, da sauran jama'a, “Aikin nan babba ne, mai yawa kuma, ga shikuwa, muna rarrabe a kan garun nesa da juna. 20Duk inda kuka ji an busa ƙaho, sai ku taru a wurin. Allahnmu zai yi yaƙi dominmu.” 21Haka kuwa muka yi aikin, rabinmu na riƙe da māsu tun daga wayewar gari har zuwa fitowar taurari.
22A wannan lokaci kuma na ce wa jama'a, kowane mutum tare da baransa ya kwana a Urushalima domin a yi tsaro da dare, da safe kuma a kama aiki. 23Saboda haka ni, da 'yan'uwana, da barorina, da matsaran da suke tare da ni, ba wanda ya tuɓe tufafinsa. Kowa yana riƙe da makami.
Currently Selected:
Neh 4: HAU
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979