YouVersion Logo
Search Icon

Neh 5

5
An Hana Ba da Kuɗi da Ruwa
1Sai mata da maza suka yi ta kuka ƙwarai saboda 'yan'uwansu Yahudawa. 2Akwai waɗanda suka ce, “Mu da 'ya'yanmu mata da maza muna da yawa, sai mu sami hatsi don mu ci mu rayu.”
3Waɗansu kuma suka ce, “Saboda yunwa mun jinginar da gonakinmu, da gonakin inabinmu, da gidajenmu don mu sami hatsi.”
4Akwai waɗansu kuma da suka ce, “Mun ci bashin kuɗi don mu biya haraji a kan gonakinmu, da gonakin inabinmu. 5Ga shi kuwa, mu da su dangin juna ne, 'ya'yanmu da nasu kuma ɗaya ne, duka da haka muna tilasta wa 'ya'yanmu mata da maza su zama bayi. Har ma waɗansu daga cikin 'ya'yanmu mata an riga an bautar da su, amma ba mu da iko mu ce kome, domin gonakinmu da gonakin inabinmu suna a hannun waɗansu mutane.”
6Ni Nehemiya na husata ƙwarai, sa'ad da na ji kukansu da wannan magana. 7#Fit 22.25; L.Fir 25.35-37; M.Sh 23.19,20 Sai na yi shawara a zuciyata, na yi wa manya da shugabanni faɗa, na ce musu, “Kuna musguna wa 'yan'uwanku da yake kuna ba su rance da ruwa.”
Sa'an nan na kira babban taro saboda su. 8Na ce musu, “Da iyakacin ƙoƙarinmu mun fanshi 'yan'uwanmu Yahudawa waɗanda aka sayar wa al'ummai, amma ga shi, kuna tilasta wa 'yan'uwanku su sayar da kansu ga 'yan'uwansu.” Sai suka yi tsit, suka rasa abin da za su ce.
9Na kuma ce musu, “Abin da kuke yi ba shi da kyau. Ya kamata ku yi tsoron Allah don ku hana al'ummai, abokan gabanmu, yi mana ba'a. 10Ni ma da 'yan'uwana da barorina muna ba da rancen kuɗi da hatsi. Sai mu daina sha'anin ba da rance da ruwa. 11Yau sai ku mayar musu da gonakinsu, da gonakin inabinsu, da na zaitunsu, da gidajensu, da kashi ɗaya bisa ɗari na kuɗi, da na hatsi, da na ruwan inabi, da na mai, waɗanda kuka karɓa a wurinsu.”
12Sa'an nan suka ce, “Za mu mayar musu da waɗannan abubuwa, ba kuwa za mu bukaci wani abu a gare su ba. Za mu yi abin da ka faɗa.”
Sai na kira firistoci su rantsar da su, cewa za su yi yadda suka alkawarta. 13Sai kuma na kakkaɓe hannuna, na ce, “Duk wanda ya karya wannan alkawari, haka Allah zai kakkaɓe shi daga gidansa da aikinsa. Allah zai kakkaɓe shi, ya wofintar da shi.”
Sai dukan taron suka amsa, “Amin, amin.” Suka kuma yabi Ubangiji. Suka kuwa cika alkawarin da suka yi.
Rashin Sonkan Nehemiya
14Tun kuma lokacin da na yi mulkin ƙasar Yahuza, a shekara ta ashirin zuwa shekara ta talatin da biyu ta sarautar sarki Artashate, shekara goma sha biyu ke nan, ni ko 'yan'uwana, ba wanda ya karɓi albashin da akan ba mai mulki. 15Waɗanda suka riga ni mulki sun nawaita wa mutane. Sun yi ta karɓar abinci da ruwan inabi daga gare su, banda shekel arba'in kowace rana domin abinci da ruwan inabi. Har ma barorin masu mulki sun nawaya wa mutane. Amma ni ban yi haka ba, saboda ina tsoron Allah. 16Na mai da hankali ga aikin garu, ban samar wa kaina gonaki ba. Barorina duka suka haɗa kai da ni a kan aikin gini. 17Duk da haka akwai Yahudawa da shugabanni ɗari da hamsin waɗanda suke cin abinci a teburina, banda waɗanda sukan zo wurinmu daga al'umman da suke kewaye da mu. 18Ga abincin da ake shiryawa kowace rana, sa ɗaya, da tumaki shida kyawawa, da kuma kaji. A kowace rana ta goma akan kawo salkunan ruwan inabi masu yawa, amma duk da haka ban karɓi albashin da akan ba mai mulki ba, domin wahala ta yi wa mutane yawa. 19Ya Allahna, ka tuna da alherin da na yi wa mutanen nan.

Currently Selected:

Neh 5: HAU

Highlight

Copy

Compare

Share

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in