YouVersion Logo
Search Icon

Neh 3

3
An Raba wa Mutane Wuraren da Za su Gina
1Eliyashib, babban firist kuwa, tare da 'yan'uwansa firistoci, suka tashi suka gina Ƙofar Tumaki. Suka tsarkake ta, suka sa mata ƙyamarenta. Suka tsarkake garun zuwa Hasumiyar Ɗari da Hasumiyar Hananel.
2Mutanen Yariko suka kama gini kusa da shi.
Sai kuma Zakkur ɗan Imri ya kama gini kusa da na mutanen Yariko.
3Iyalin Hassenaya suka gina Ƙofar Kifi, suka kafa katakanta, suka sa ƙyamarenta, da sandunan ƙarfe na kulle ƙofofinta.
4Kusa da su kuma, sai Meremot ɗan Uriya, wato jīkan Hakkoz ya yi gyare-gyare.
Kusa da shi kuma sai Meshullam ɗan Berikiya jikan Meshezabel ya yi gyare-gyare.
Kusa da shi kuma sai Zadok ɗan Ba'ana ya yi gyare-gyare.
5Kusa da Zadok kuwa mutanen Tekowa suka yi nasu gyare-gyare, amma manyansu ba su sa hannu ga aikin shugabanninsu ba.
6Yoyada ɗan Faseya, da Meshullam ɗan Besodeya, suka gyara Tsohuwar Ƙofa, suka kafa katakanta, suka sa ƙyamarenta, da sandunan ƙarfe na kulle ƙofofinta.
7Kusa da su kuma sai Melatiya Bagibeyone, da Yadon Bameronote, da mutanen Gibeyon, da na Mizfa waɗanda suke a ƙarƙashin mulkin Yammacin Kogin Yufiretis suka yi gyare-gyare.
8Kusa da su kuma sai Uzziyel ɗan Harhaya, maƙerin zinariya, ya yi gyare-gyare.
Kusa da Uzziyel kuma sai Hananiya, ɗaya daga cikin masu yin turare, ya yi gyare-gyare. Suka gyare Urushalima har zuwa Garu Mai Faɗi.
9Kusa da su kuma sai Refaya ɗan Hur, mai mulkin rabin yankin Urushalima, ya yi gyare-gyare.
10Kusa da Refaya kuma, sai Yedaiya ɗan Harumaf ya yi gyare-gyare daura da gidansa.
Kusa da Yedaiya sai Hattush ɗan Hashabnaiya ya yi gyare-gyare.
11Malkiya ɗan Harim, da Hasshub ɗan Fahat-mowab suka gyara wani sashi da kuma Hasumiyar Tanderu.
12Kusa da su kuma, sai Shallum ɗan Hallohesh mai mulkin rabin yankin Urushalima ya yi gyare-gyare tare da 'ya'yansa mata.
13Hanun da mazaunan Zanowa suka gyara Ƙofar Kwari. Sun gina ta, suka sa ƙyamarenta, da sandunan ƙarfe na kulle ƙofofinta, da ƙyamarenta, suka gyara garun kamu dubu, har zuwa Ƙofar Juji.
14Malkiya ɗan Rekab, mai mulkin yankin Bet-akkerem, ya gyara Ƙofar Juji. Ya gina ta, ya sa ƙyamarenta da sandunan ƙarfe na kulle ƙofofinta.
15Sai Shallum ɗan Kolhoze, mai mulkin yankin Mizfa ya gyara Ƙofar Maɓuɓɓuga, ya gina ta, ya rufe ta, ya sa ƙyamarenta, da sandunan ƙarfe na kulle ƙofofinta. Ya kuma gina garun Tafkin Siluwam na gonar sarki, har zuwa matakan da suka gangaro daga Birnin Dawuda.
16Bayansa kuma Nehemiya, ɗan Azbuk, mai mulkin yankin Bet-zur ya yi gyare-gyare, har zuwa wani wuri daura da kabarin Dawuda, har zuwa haƙaƙƙen tafki da gidan masu tsaro.
Lawiyawan da Suka Yi Aikin Garu
17Waɗannan Lawiyawa sun yi gyare-gyare a ƙarƙashin shugabancin Rehum ɗan Bani.
Kusa da su kuma, sai Hashabiya mai mulkin rabin yankin Kaila, ya yi gyare-gyare domin yankinsa.
18Bayansa kuma, sai 'yan'uwansu suka yi gyare-gyare a ƙarƙashin shugabancin Bawwai ɗan Henadad, mai mulkin rabin yankin Kaila.
19Kusa da su kuma sai Ezer ɗan Yeshuwa, mai mulkin Mizfa, ya gyara wani sashi a gaban gidan makamai a wajen kusurwa.
20Bayansa kuma, Baruk ɗan Zabbai, ya gyara wani sashi daga wajen kusurwar, har ya zuwa ƙofar gidan Eliyashib babban firist.
21Bayansa kuma Meremot ɗan Uriya, ɗan Hakkoz, ya gyara wani sashi daga ƙofar gidan Eliyashib, zuwa ƙarshen gidan.
Firistocin da Suka Yi Aikin Garu
22Bayansa kuma sai firistoci, mutanen filin kwari, suka yi gyare-gyare.
23Bayansu kuma Biliyaminu da Hasshub suka yi gyara daura da gidansu. Bayansu kuma Azariya, ɗan Ma'aseya, wato jikan Ananiya, ya yi gyara kusa da gidansa.
24Bayansa kuma Binnuyi, ɗan Henadad, ya gyara wani sashi daga gidan Azariya zuwa kusurwar garun.
25Falal ɗan Uzai, ya gyara wani sashi daga kusurwar da hasumiyar benen gidan sarki a wajen shirayin matsara.
Bayansa kuma sai Fedaiya ɗan Farosh ya yi gyare-gyare. 26Ma'aikatan Haikali da suke zaune a Ofel suka yi gyare-gyare zuwa wani wuri daura da Ƙofar Ruwa wajen gabas, har zuwa wata doguwar hasumiya.
Sauran Masu Gini
27Bayansu kuma mutanen Tekowa suka gyara wani sashi daura da babbar doguwar hasumiya, har zuwa garun Ofel.
28Daga Ƙofar Dawaki, firistoci suka yi gyare-gyare, kowa ya yi gyara daura da gidansa.
29Bayansu kuma Zadok, ɗan Immer, ya gyara wani sashi daura da gidansa.
Bayansa kuma Shemaiya, ɗan Shekaniya, mai tsaron Ƙofar Gabas ya yi gyare-gyare.
30Bayansa kuma Hananiya ɗan Shelemiya, da Hanun, ɗa na shida na Zalaf, suka gyara wani sashi, kashi na biyu.
Bayansu kuma Meshullam, ɗan Berikiya, ya gyara wani sashi daura da gidansa.
31Bayansa kuma, Malkiya, ɗaya daga cikin maƙeran zinariya ya yi gyare-gyare, har zuwa gidan ma'aikatan Haikali da na 'yan kasuwa, daura da Ƙofar Taruwa, har zuwa soron bene a wajen kusurwa.
32Maƙeran zinariya da 'yan kasuwa suka gyara wani sashi tsakanin soron bene daga kusurwa da Ƙofar Tumaki.

Currently Selected:

Neh 3: HAU

Highlight

Copy

Compare

Share

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in