YouVersion Logo
Search Icon

Ayu 5

5
1“Ka yi kira, ya Ayuba, ka gani, ko wani zai amsa!
Akwai wani mala'ika da za ka juya zuwa gare shi?
2Ba shi da amfani ka dami kanka
Har ka mutu, saboda tsarguwa, gama wannan wawanci ne,
Da aikin rashin hankali.
3Na ga waɗansu wawaye waɗanda ake gani kamar suna zaune lafiya,
Amma nan da nan sai na la'anci gidajensu.
4Ko kaɗan, 'ya'yansu maza ba za su taɓa zama lafiya ba.
Ba wanda zai tsaya musu a ɗakin shari'a.
5Mayunwata za su ci amfanin gonar wawa,
Har da hatsin da yake girma cikin ƙayayuwa,
Waɗanda suke jin ƙishirwa za su ji ƙyashin dukiyarsa.
6Zunubi ba ya tsirowa daga ƙasa,
Haka ma wahala ba ta tsirowa daga ƙasa.
7Ai, an haifi mutum domin wahala ne,
Tabbatacce ne kamar yadda tartsatsin wuta suke tashi.
8“In da ni ne kai, da sai in juya wurin Allah,
In kai ƙarata a wurinsa.
9Ba za mu iya fahimtar manyan abubuwa da yake yi ba,
Al'ajabansa kuwa ba su da iyaka.
10Yakan aiko da ruwan sama,
Ya shayar da gonaki.
11I, Allah ne yake ɗaukaka masu tawali'u,
Shi yake kuɓutar da dukan waɗanda suke makoki.
12 # 1Kor 3.19 Yakan birkitar da shirye-shiryen masu wayo.
13Yakan sa wa masu wayo tarko cikin dabarunsu,
Har ba za su yi nasara a dukan abin da suke yi ba.
14Da rana sukan yi karo da duhu,
Ko da tsakar rana ma lalube suke kamar ana duhu.
15Amma Allah yakan ceci matalauta daga mutuwa,
Yakan kuma ceci masu bukata daga zalunci.
16Yakan sa matalauta su sa zuciya,
Ya sa mugaye su yi shiru.
17 # K.Mag 3.11,12; Ibr 12.5,6 “Mai farin ciki ne mutumin da Allah ya hora,
Kada ka tsargu sa'ad da ya tsauta maka.
18 # Yush 6.1 Allah yakan yi maganin raunin da ya yi maka,
Ciwon da ya ji maka da hannunsa,
Da hannunsa yakan warkar.
19Yakan tsare ka daga cuta sau shida har sau bakwai,
Ba muguntar da za ta taɓa ka.
20Yakan kiyaye ka da rai a lokacin yunwa,
A yaƙi kuma yakan tsare ka daga mutuwa.
21Allah yakan kuɓutar da kai daga ƙarairayi da ɓata suna,
Yakan cece ka daga hallaka.
22Aikin kama-karya da yunwa za su zama abin dariya a gare ka,
Ba kuwa za ka ji tsoron namomin jeji ba.
23Ba za a sami duwatsu a gonakin da kake nomawa ba,
Mugayen namomin jeji ba za su far maka ba.
24Sa'an nan za ka zauna lafiya a alfarwanka,
A sa'ad da ka dubi tumakinka, za ka tarar suna nan lafiya.
25'Ya'yanka za su yi yawa kamar ciyawa,
Kamar yadda alkama take a lokacin kakarta.
26Haka kai ma za ka rayu, har ka tsufa da kyakkyawan tsufa.
27Kai, Ayuba, mun koyi wannan don mun daɗe muna nazari,
Gaskiya ce, don haka ka yarda da wannan.”

Currently Selected:

Ayu 5: HAU

Highlight

Copy

Compare

Share

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in