YouVersion Logo
Search Icon

Ayu 4

4
Elifaz Ya Tsauta wa Ayuba
1Elifaz ya yi magana.
2“Ayuba, za ka ji haushi in na yi magana?
Ba zan iya kannewa, in yi shiru ba.
3Ka koya wa mutane da yawa,
Ka kuma ƙarfafa hannuwan marasa ƙarfi.
4Idan wani ya yi tuntuɓe,
Ya gaji, ya rasa ƙarfi,
Kalmominka suka ƙarfafa zuciyarsa,
Har ya iya tsayawa kyam.
5Yanzu naka lokacin wahala ya zo,
Kai kuwa ka rikice, ka kasa ɗaurewa,
6Kana yi wa Allah sujada,
Ba wani laifi a zamanka,
Ya kamata ka amince ka sa zuciya.
7“Yanzu fa sai ka yi tunani.
Ka faɗi bala'i ɗaya wanda ya taɓa fāɗa wa adalin mutum.
8Na taɓa ganin mutane suna huɗe gonar mugunta,
Suna shuka mugunta,
Suka kuwa girbe mugunta.
9A cikin fushinsa Allah yakan hallaka su kamar hadiri.
10Mugaye sukan yi ruri suna gurnani kamar zakoki,
Amma Allah yakan sa su yi tsit,
Ya kakkarya haƙoransu.
11Kamar zakoki da ba su da abin da za su kashe su ci,
Haka nan za su mutu, 'ya'yansu kuwa su warwatse duka.
12“Wata rana wani saƙo ya zo a hankali,
Har da ƙyar nake iya ji,
13 # Ayu 33.15 Kamar wani irin mafarki mai razanarwa yake,
Wanda ya hana ni jin daɗin barcina.
14Na yi rawar jiki ina makyarkyata,
Duk jikina yana ta ɓare-ɓare don tsoro.
15Wata iska marar ƙarfi ta taɓa fuskata,
Sai fatar jikina ta yanƙwane saboda fargaba.
16Na ga wani abu can yana tsaye,
Na zura ido, amma ban san kowane irin abu ba ne,
Ina cikin wannan hali sai na ji murya,
17Ta ce, ‘Mutum yana iya zama adali a gaban Allah?
Akwai kuma wanda yake mai tsarki a gaban Mahaliccinsa?
18Allah ba ya amince wa barorinsa na cikin sammai,
Yakan sami laifi a wurin mala'ikunsa.
19Ta ƙaƙa zai amince da talikinsa wanda aka yi da ƙasa,
Abin da yake na ƙura, ana kuwa iya murƙushe shi kamar asu.
20Mai yiwuwa ne mutum yana raye da safe
Amma ya mutu ba a sani ba kafin maraice.
21Duk abin da ya mallaka an ɗauke,
Duk da haka ya mutu cikin rashin hikima.’ ”

Currently Selected:

Ayu 4: HAU

Highlight

Copy

Compare

Share

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in