Ayu 26
26
Ayuba Ha Hurta Sarautar Allah
1Ayuba ya amsa.
2“Kai ne mai taimakon marar ƙarfi,
Kai ne mai ceton rarrauna!
3Kai ne kake ba marar hikima shawara,
Kai kake sanar da ilimi mai ma'ana a wadace!
4Kana tsammani wane ne zai ji maganganunka duka?
Wane ne ya iza ka ka yi irin wannan magana?
5“Lahira tana rawa,
Mazaunanta suna rawar jiki don tsoro.
6Lahira tsirara take a gaban Allah,
Haka kuma Halaka take a gaban Allah.
7Allah ne ya shimfiɗa arewa a sarari kurum,
Ya rataya duniya ba bisa kan kome ba.
8Allah ne ya cika gizagizai masu duhu da ruwa,
Girgijen kuwa bai kece ba.
9Ya rufe kursiyinsa, ya shimfiɗa girgije a kansa.
10Ya shata da'ira a kan fuskar teku,
A kan iyakar da take tsakanin haske da duhu.
11Ginshiƙan samaniya sun girgiza,
Sun firgita saboda tsautawarsa.
12Ta wurin ƙarfinsa ya kwantar da teku,
Da saninsa ya hallaka dodon ruwan nan, wato Rahab.
13Da numfashinsa ya sa sararin sama ya yi garau,
Ikonsa ne kuma ya sha zarar macijin nan mai gudu.
14Amma waɗannan kaɗan ne kawai daga cikin al'amuransa.
Ɗan ƙis kaɗai muke ji a kansa.
Amma wa zai iya fahimtar ikon tsawarsa?”
Currently Selected:
Ayu 26: HAU
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979