YouVersion Logo
Search Icon

Ayu 25

25
Bildad Bai Yarda Allah Zai Baratar da Mutum Ba
1Bildad ya amsa.
2“Allah mai iko ne, duka sai a ji tsoronsa,
A samaniya yake tafiya da mulkinsa da salama.
3Akwai wanda zai iya ƙidaya mala'ikun da suke masa hidima?
Akwai wurin da hasken Allah bai haskaka ba?
4Akwai wanda ya isa ya zama adali,
Ko mai tsarki a gaban Allah?
5Hasken wata ba haske ba ne a gare shi,
Ko taurari ma ba su da tsarki a gabansa.
6To, mutum fa? Ai, wannan tsutsa ne, ɗan ƙwaro kawai.
Me mutum ya daɗa a gaban Allah?”

Currently Selected:

Ayu 25: HAU

Highlight

Copy

Compare

Share

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in