YouVersion Logo
Search Icon

Ayu 27

27
Ayuba Ya Bayyana Rabon Mugaye
1Ayuba ya amsa.
2“Na rantse da Allah Mai Iko Dukka,
Wanda ya ƙwace mini halaliyata,
Wanda ya ɓata mini rai.
3Muddin ina numfashi,
Ruhun Allah kuma yana cikin hancina
4Bakina ba zai faɗi ƙarya ba,
Harshena kuma ba zai hurta maganganun yaudara ba.
5Allah ya sawwaƙa in ce kun yi daidai,
Har in mutu ba zan daina tsare mutuncina ba.
6Ina riƙe da adalci kam, ba kuwa zan sake shi ba,
Zuciyata ba ta zarge ko ɗaya daga cikin kwanakin raina ba.
7“Bari maƙiyina ya zama kamar mugun mutum,
Wanda ya tashi gāba da ni ya zama kamar marar adalci.
8Wace sa zuciya take ga marar tsoron Allah?
Sa'ad da Allah ya datse shi, ya ɗauke ransa?
9Allah kuwa zai ji kukansa sa'ad da wahala ta same shi?
10Ko Mai Iko Dukka zai zama abin farin ciki a gare shi?
Ko zai yi kira ga Allah a kowane lokaci?
11“Zan koya muku zancen ikon Allah,
Abin da yake na wajen Mai Iko Dukka ba zan ɓoye ba.
12Ga shi kuwa, dukanku kun gani da kanku,
Me ya sa kuka zama wawaye?
13“Wannan shi ne rabon mugaye daga wurin Allah,
Gādo ne kuma wanda azzalumai za su karɓa daga wurin Mai Iko Dukka.
14Idan 'ya'yansu sun riɓaɓɓanya za su zama rabon takobi,
Zuriyarsu kuwa ba za su sami isasshen abinci ba.
15Waɗanda suka tsira, annoba za ta kashe su,
Matansu ba za su yi makokin mutuwarsu ba.
16Ko da yake sun tsibe azurfa kamar turɓaya,
Sun tara tufafi kamar ƙasa,
17Za su tara, amma adalai za su sa,
Marasa laifi ne za su raba azurfar.
18Sun gina gidajensu kamar saƙar gizo-gizo,
Kamar bukkar mai tsaro.
19Attajirai za su kwanta, amma daga wannan shi ke nan,
Za su buɗe ido su ga dukiyan nan ba ta.
20Razana za ta auka musu kamar rigyawa.
Da dare iska za ta tafi da su.
21Iskar gabas za ta fauce su su tafi,
Ta share su ta raba su da wurin zamansu.
22Za ta murɗe su ba tausayi,
Hakika za su yi ƙoƙari su tsere daga ikonsa,
Sai su yi ƙundumbala.
23Kowa zai tafa hannu yă yi musu tsaki har su tashi daga wurin da suke.”

Currently Selected:

Ayu 27: HAU

Highlight

Copy

Compare

Share

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in