YouVersion Logo
Search Icon

Eze 2

2
Kiran Ezekiyel
1Sai ya ce mini, “Ɗan mutum, ka tashi tsaye, zan yi magana da kai.” 2Da ya yi magana da ni, sai Ruhu ya sauko a kaina, ya ta da ni tsaye, sa'an nan na ji yana magana da ni. 3Ya ce mini, “Ɗan mutum na aike ka zuwa wurin jama'ar Isra'ila, al'umma mai tayarwa, waɗanda suka tayar mini. Su da ubanninsu suna yi ta yi mini laifi har yau. 4Su mutane ne marasa kunya, masu taurinkai. Ga shi kuwa, na aike ka gare su, ka ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Runduna ya faɗa.’ 5Ko su ji, ko kada su ji, gama su masu tayarwa ne, amma za su sani akwai annabi a cikinsu.
6“Kai ɗan mutum, kada ka ji tsoronsu, kada kuma ka ji tsoron maganganunsu, ko da ya ke ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya sun kewaye ka, kana kuma zaune tare da kunamai. Kada ka ji tsoron maganganunsu ko ka karai saboda irin kallon da za su yi maka, gama su 'yan tawaye ne. 7Za ka faɗa musu maganata, ko su ji, ko kada su ji, gama su 'yan tawaye ne.
8“Amma kai, ya ɗan mutum, ka ji abin da zan faɗa maka, kada ka zama mai tayarwa kamar 'yan tawayen nan. Sai ka buɗe bakinka, ka ci abin da zan ba ka.” 9#W.Yah 5.1 Da na duba, sai ga hannu yana miƙo mini littafi. 10Ya buɗe littafin a gabana, akwai rubutu ciki da baya. Ba abin da aka rubuta sai maganganun baƙin ciki, da makoki, da kaito.

Currently Selected:

Eze 2: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in