YouVersion Logo
Search Icon

Eze 1

1
Ezekiyel Ya Ga Wahayi na Ɗaukakar Ubangiji
1 # W.Yah 19.11 A ranar biyar ga watan huɗu, a shekara ta talatin, ina cikin waɗanda aka kai su bautar talala, muna kusa da kogin Kebar, sai aka buɗe mini sammai, na kuwa ga wahayi na ɗaukakar Allah. 2#2Sar 24.10-16; 2Tar 36.9,10 A kan rana ta biyar ga watan, a shekara ta biyar da aka kai sarki Yekoniya bautar talala, 3Ubangiji ya yi magana da Ezekiyel, firist, ɗan Buzi, a ƙasar Kaldiyawa, kusa da kogin Kebar. Ikon Ubangiji yana bisa kansa.
4Da na duba, sai ga hadiri mai iska ya taso daga wajen arewa, da wani babban girgije da haske kewaye da shi, da wuta tana ta ci falfal. A tsakiyar wutar wani abu yana walƙiya kamar tagulla. 5#W.Yah 4.6 Daga tsakiya wutar, sai ga kamannin waɗansu talikai su huɗu. Ga irin kamanninsu, suna kama da mutane. 6Amma kowannensu yana da fuskoki huɗu, da fikafikai huɗu. 7Ƙafafunsu miƙaƙƙu ne, tafin sawayensu yana kama da na maraƙi, suna walƙiya kamar gogaggiyar tagulla. 8Suna kuma da hannuwa kamar na mutane a ƙarƙarshin fikafikansu huɗu. Ga yadda fuskoki da fikafikan talikai huɗu ɗin suke. 9Fikafikansu suna taɓa juna, kowannensu ya miƙe gaba, ba su juyawa sa'ad da suke tafiya.
10 # Eze 10.14; W.Yah 4.7 Kamannin fuskokinsu, su huɗu ɗin, kowannensu yana da fuska irin ta mutum a gaba, da fuska irin ta zaki a dama, da fuska irin ta bijimi a hagu, da fuska irin ta gaggafa a baya. 11Suka kuma buɗe fikafikansu sama. Kowane taliki yana taɓa fiffiken ɗan'uwansa da fikafikansa biyu, da kuma fikafikansa biyu yake rufe jikinsa. 12Kowannensu kuwa ya miƙe gaba sosai, zuwa inda ruhu ya bishe shi. Sun tafi ba waiwaye.
13 # W.Yah 4.5 A tsakiyar talikan akwai wani abu mai kama da garwashin wuta, kamar jiniyoyi kuma suna kai da kawowa a tsakanin talikan, wutar kuwa tana haskakawa. Daga cikin wutar kuma, sai ga walƙiya tana fitowa. 14Talikan kuma suka yi ta giftawa suna kai da kawowa kamar walƙiya.
15 # Eze 10.9-13 Da na dubi talikan, sai na ga ƙafafu huɗu kamar na keke a ƙasa kusa da talikan. Ɗaya domin kowane taliki. 16Ga kamannin ƙafafun da yadda aka yi su. Suna ƙyalƙyali kamar duwatsu masu daraja. Dukansu huɗu fasalinsu ɗaya ne. An yi su kamar wata ƙafa tana cikin wata ƙafa. 17Sa'ad da suke tafiya, suna tafiya a kowane waje, ba sai sun juya ba. 18#W.Yah 4.8 Akwai waɗansu ƙarafa kamar zobe, da idanu kuma tantsai kewaye da ƙafafun.
19Duk sa'ad da talikan suka motsa, sai kuma ƙafafun su motsa tare da su. Idan kuma talikan suka ɗaga sama, sai ƙafafun su ɗaga tare da su. 20Duk inda ruhu ya nufa, sai talikan su bi, sai kuma ƙafafun su tafi tare da su, gama ruhun talikan yana cikin ƙafafun. 21Idan talikan sun motsa, sai ƙafafun kuma su motsa. Idan sun tsaya cik, sai su ma su tsaya. Idan kuma talikan sun ɗaga sama, sai ƙafafun su ɗaga sama tare da su, gama ruhun talikan yana cikin ƙafafun.
22 # W.Yah 4.6 Sama da talikan akwai kamannin al'arshi mai walƙiya kamar madubi. 23A ƙarƙashin al'arshin fikafikansu sun miƙe kyam daura da juna. Kowane taliki yana da fikafikai biyu da su yake rufe jikinsa. 24#W.Yah 1.4-15; 19.6 Sa'ad da suke tafiya, sai na ji motsin fikafikansu kamar amon ruwa, kamar kuma muryar tsawar Maɗaukaki, kamar hayaniyar runduna. Idan sun tsaya cik, sai su saukar da fikafikansu. 25Sai aka ji murya ta fito daga saman al'arshi ɗin.
26 # Eze 10.1; W.Yah 4.2,3 A saman al'arshin akwai wani abu mai kamar kursiyin sarauta da aka yi da yakutu. Akwai wani kamar mutum yana zaune a kan abin nan mai kama da kursiyin sarauta. 27#Eze 8.2 Daga kwankwasonsa zuwa sama yana walƙiya kamar tagullar da aka kewaye ta da wuta. Daga kwankwasonsa zuwa ƙasa yana haskakawa kamar wuta. 28Kamar kamannin bakan gizo a cikin gizagizai a ranar da aka yi ruwan sama, haka nan kamannin hasken da yake kewaye da shi yake. Wannan shi ne kamannin kwatancin ɗaukakar Ubangiji. Sa'ad da na gani, sai na faɗi rubda ciki, na ji muryar wani tana magana.

Currently Selected:

Eze 1: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in