Eze 3
3
1 #
W.Yah 10.9,10 Sai ya ce mini, “Ɗan mutum ka ci abin da aka ba ka. Ka ci wannan littafi, sa'an nan ka tafi ka yi wa mutanen Isra'ila magana.”
2Sai na buɗe bakina, sa'an nan ya ba ni littafin in ci. 3Ya kuma ce mini, “Ɗan mutum, ka ci littafin nan da na ba ka, ka cika tumbinka da shi.” Sai na ci littafin, na ji shi a bakina da zaƙi kamar zuma.
4Ya kuma ce mini, “Ɗan mutum ka tafi wurin mutanen Isra'ila ka faɗa musu maganata. 5Gama ba a aike ka a wurin mutane waɗanda suke da baƙon harshe wanda ba ka sani ba, amma zuwa mutanen Isra'ila, 6ba wurin waɗansu mutane dabam waɗanda suke da baƙon harshe mai wuya ba, wato harshen da ba ka sani ba. Da na aike ka wurin irin mutanen nan da za su ji. 7Amma mutanen Isra'ila ba za su ji ka ba, ba su kuwa da nufi su ji ni, gama suna da taurinkai da taurin zuciya. 8Ga shi, na sa fuskarka da goshinka su zama da tauri kamar nasu. 9Kamar yadda lu'ulu'u ya fi ƙanƙarar dutse ƙarfi, haka nan na sa goshinka ya zama. Kada ka ji tsoronsu, ko kuwa ka karai saboda irin kallon da za su yi maka, gama su 'yan tawaye ne.”
10Ya kuma ce mini, “Ɗan mutum, sai ka ji, ka karɓi dukan maganata da zan faɗa maka. 11Sa'an nan ka tafi wurin mutanenka waɗanda suke cikin bautar talala, ka faɗa musu, ko su ji, ko kada su ji.”
12Sa'an nan Ruhu ya ɗaga ni, sai na ji murya a bayana, kamar babban motsi, tana cewa, “Yabo ga ɗaukakar Ubangiji a kursiyinsa.” 13Na kuma ji amon fikafikan talikan ne sa'ad da suka taɓa junansu, da kuma amon ƙafafun da suke kusa da talikan, da amon babban motsi. 14Sai Ruhu ya ɗaga ni, ya kuma tafi da ni, na kuwa tafi da baƙin ciki, ina jin zafi a ruhuna. Ikon Ubangiji yana tare da ni da ƙarfi. 15Na zo wurin 'yan bautar talala a Telabib, waɗanda suke bakin kogin Kebar. Na zauna tare da su kwana bakwai, ina ta mamaki.
Ezekiyel Ya Zama Mai Tsaron Isra'ila
(Eze 33.1-9)
16A ƙarshen kwana bakwai ɗin, sai Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce, 17“Ɗan mutum, na maishe ka mai tsaron gidan Isra'ila. Sa'ad da ka ji magana daga bakina, sai ka faɗakar da su a madadina. 18Idan na ce wa mugu, ‘Lalle za ka mutu,’ kai kuwa ba ka faɗakar da shi a kan mugayen ayyukansa don ka ceci ransa ba, wannan mugun mutum zai mutu cikin zunubinsa, amma zan nemi hakkin jininsa a hannunka. 19Amma idan ka faɗakar da mugu, ya kuwa ƙi barin muguntarsa, zai mutu cikin zunubinsa, kai kam ka kuɓuta.
20“Idan kuma adali ya bar adalci sa'an nan ya aikata zunubi, ni kuwa na sa abin tuntuɓe a gabansa, zai mutu. Zai mutu saboda zunubinsa domin ba ka faɗakar da shi ba. Ba za a tuna da ayyukansa na adalci waɗanda ya yi ba, amma zan nemi hakkin jininsa a hannunka. 21Amma idan ka faɗakar da adali, kada ya aikata zunubi, shi kuwa bai aikata zunubi ba, hakika zai rayu domin ya ji faɗakar, kai kuma ka kuɓuta.”
Annabi Ya Zama Bebe
22Ikon Ubangiji yana tare da ni, Ubangiji kuwa ya ce mini, “Tashi, ka tafi ka tsaya a fili, a can zan yi magana da kai.”
23Sai na tashi na tafi na tsaya a fili, sai ga ɗaukakar Ubangiji a wurin, a tsaye kamar ɗaukakar da na gani a bakin kogin Kebar. Sai na fāɗi rubda ciki. 24Ruhu kuwa ya sauko a kaina, ya ta da ni tsaye. Sai ya yi magana da ni, ya ce, “Ka tafi, ka kulle kanka cikin gida. 25Ya ɗan mutum, za a ɗaure ka da igiyoyi don kada ka tafi cikin jama'a. 26Ni kuwa zan sa harshenka ya manne wa dasashinka don ka zama bebe, ka kasa tsauta musu, gama su 'yan tawaye ne. 27Amma sa'ad da na yi magana da kai, zan buɗe bakinka, kai kuwa za ka yi musu magana, ka ce, ‘Ubangiji ya ce, wanda zai ji, to, ya ji, wanda kuma zai ƙi ji, ya ƙi ji,’ gama su 'yan tawaye ne.”
Currently Selected:
Eze 3: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979