YouVersion Logo
Search Icon

Fit 39

39
Yin Tufafin Firistoci
(Fit 28.1-43)
1An yi wa firistoci tufafi masu kyau na shuɗi, da na shunayya, da na mulufi, domin yin aiki a Wuri Mai Tsarki. Suka yi wa Haruna tsarkakan tufafi kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.
2Ya yi falmaran da zinariya, da shuɗi, da shunayya, da mulufi, da lallausan lilin. 3An kuma buga zinariya fake-fake, suka yanyanka ta zare-zare don su yi saƙa da ita tare da zane na shuɗi, da na shunayya, da na mulufi, da na lallausan lilin, aikin gwani mai fasaha. 4Suka yi wa falmaran kafaɗu, sa'an nan suka haɗa su a gefenta biyu na sama. 5Gwanin masaƙi ya saƙa abin ɗamarar falmaran. Da irin kayan da aka saƙa falmaran ne aka saƙa abin ɗamarar, wato da zinariya, da shuɗi, da shunayya, da mulufi, da zaren lallausan lilin kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa. 6Sai aka gyaggyarta duwatsu masu daraja aka jera su cikin tsaiko na zinariya. Aka zana sunayen 'ya'yan Isra'ila a kan duwatsun kamar yadda akan yi hatimi. 7Aka sa su a kan kafaɗun falmaran don su zama duwatsun tunawa da Isra'ila kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.
8Aka kuma yi ƙyallen maƙalawa a ƙirji da gwaninta kamar yadda aka yi wa falmaran aiki da zinariya, da shuɗi, da shunayya, da mulufi, da lallausan lilin. 9Ƙyallen maƙalawa a ƙirji murabba'i ne, aka ninka shi biyu, tsawonsa da fāɗinsa kamu ɗaya ɗaya ne. 10Sai suka sa jeri huɗu na duwatsu masu daraja a bisansa. A jeri na fari aka sa yakutu, da tofaz, da zumurrudu. 11A jeri na biyu aka sa turkos, da saffir, da daimon. 12A jeri na uku aka sa yakinta, da idon mage, da ametis. 13A jeri na huɗu aka sa beril, da onis, da yasfa. Aka sa su cikin tsaiko na zinariya. 14An zana sunayen 'ya'yan Isra'ila goma sha biyu a kan duwatsu masu daraja kamar yadda akan yi hatimi. 15Sai suka yi tukakkun sarƙoƙi na zinariya tsantsa a kan ƙyallen maƙalawa a ƙirji. 16Suka yi tsaiko biyu na zinariya da ƙawane biyu na zinariya. Sai suka sa ƙawanen nan biyu a gefe biyu na ƙyallen maƙalawa a ƙirji. 17Suka kuma zura sarƙoƙin nan biyu na zinariya a ƙawanen nan biyu na zinariya na gyaffan ƙyallen maƙalawa a ƙirji. 18Sai suka maƙala waɗancan bakin sarƙoƙin zinariya a tsaikon nan biyu, sa'an nan suka rataya su a kafaɗun falmaran daga gaba. 19Suka kuma yi ƙawane biyu na zinariya, suka sa su a gefe biyu na ƙyallen maƙalawa a ƙirji daga ciki kusa da falmaran. 20Suka yi waɗansu ƙawane biyu na zinariya, suka maƙala su daga ƙasa a gaban kafaɗu biyu na falmaran kusa da mahaɗin a bisa abin ɗamarar falmaran. 21Sai suka ɗaure ƙawanen ƙyallen maƙalawa a ƙirjin a ƙawanen falmaran da shuɗiyar igiya don ƙyallen maƙalawa a ƙirji ya kwanta lif a bisa kan abin ɗamarar falmaran don kada ya kwance daga falmaran, sun yi kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.
22Ya kuma saƙa taguwa ta falmaran da shuɗi duka. 23An yi wa taguwar wuyan wundi kamar sulke, aka daje wuyan don kada ya kece. 24A karbun taguwar, suka yi fasalin 'ya'yan rumman da shuɗi, da shunayya, da mulufi, da lallausan lilin. 25Suka kuma yi ƙararrawa da zinariya tsantsa, suka sa su a tsakankanin fasalin 'ya'yan rumman kewaye da karbun taguwa. 26An jera su bi da bi, wato fasalin rumman yana biye da ƙararrawa. Haka aka jera su kewaye da karbun taguwar yin aiki, kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.
27Suka saƙa zilaika da lallausan zaren lilin don Haruna da 'ya'yansa. 28Suka kuma yi rawani, da huluna, da mukurai da lallausan lilin. 29Sun kuma yi abin ɗamara da lallausan lilin mai launin shuɗi, da shunayya, da mulufi. Aka yi mata ɗinkin ado kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa. 30Suka yi allo tsattsarka da zinariya tsantsa suka zāna rubutu irin na hatimi a kansa haka, “MAI TSARKI GA UBANGIJI.” 31Suka ɗaura shi da shuɗiyar igiya a gaban rawanin kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.
Ƙarewar Aikin
32Haka kuwa aka gama dukan aiki na alfarwa ta sujada. Isra'ilawa suka yi shi kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa. 33Sai suka kawo wa Musa alfarwa da dukan kayayyakinta, wato da maratayanta, da katakanta, da sandunanta, da dirkokinta, da kwasfanta, 34da murfi na fatun raguna da na awaki, da labulen, 35da akwatin alkawari da sandunansa, da murfinsa, 36da tebur, da kayayyakinsa duka, da gurasar ajiyewa, 37da alkuki na zinariya tsantsa da fitilunsa da dukan kayayyakinsa, da man fitila, 38da bagade na zinariya, da man keɓewa, da turare mai ƙanshi, da labulen ƙofar alfarwar, 39da bagade na tagulla da ragarsa ta tagulla, da sandunansa da dukan kayayyakinsa, da daro da gammonsa, 40da labulen farfajiya da dirkokinta, da kwasfanta, da labulen ƙofarta, da igiyoyinta, da turakunta, da dukan kayayyakin yin aiki a alfarwa ta sujada, 41da tufafin ado na aiki a Wuri Mai Tsarki, wato tsarkakan tufafin Haruna firist, da tufafin 'ya'yansa maza don su yi aikin firistoci. 42Isra'ilawa sun yi dukan aiki kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa. 43Da Musa ya duba dukan aikin, ga shi kuwa, sun yi shi daidai, kamar yadda Ubangiji ya umarta, sai Musa ya sa musu albarka.

Currently Selected:

Fit 39: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in

YouVersion uses cookies to personalize your experience. By using our website, you accept our use of cookies as described in our Privacy Policy