YouVersion Logo
Search Icon

Fit 40

40
Kafawar Alfarwa ta Sujada da Keɓewarta
1Ubangiji kuwa ya ce wa Musa, 2“A kan rana ta fari ga wata na fari za ka kafa alfarwa ta sujada. 3Sai ka sa akwatin alkawari a cikinta sa'an nan ka kāre shi da labule. 4Ka shigar da tebur ɗin, ka shirya kayayyakinsa daidai. Ka kuma shigar da alkukin, ka sa fitilu a bisansa. 5Ka ajiye bagade na zinariya na ƙona turare a gaban akwatin alkawari, sa'an nan ka rataya labulen ƙofar alfarwa. 6Ka ajiye bagade na yin hadaya ta ƙonawa a gaban ƙofar alfarwa ta sujada, 7ka kuma ajiye daro tsakanin alfarwa ta sujada da bagaden, sa'an nan ka zuba ruwa a ciki. 8Sai ka yi farfajiya ka kewaye wurin sa'an nan ka rataya labulen ƙofar farfajiyar.
9“Ka ɗauki man keɓewa, ka shafa wa alfarwa da dukan abin da yake cikinta, domin ka tsarkake ta da kayayyakinta duka, za ta kuwa zama tsarkakakkiya. 10Ka shafa wa bagade na ƙona hadaya da kayayyakinsa duka man domin ka tsarkake shi, bagaden kuma zai zama mafi tsarki. 11Ka kuma shafa wa daron da gammonsa man keɓewa, da haka za ka tsarkake shi.
12“Ka kuma kawo Haruna da 'ya'yansa maza a ƙofar alfarwa ta sujada, ka yi musu wanka da ruwa. 13Sa'an nan ka sa wa Haruna tufafi tsarkaka ka shafa masa man domin ka tsarkake shi ya yi mini aiki na firist. 14Sai ka kawo 'ya'yan Haruna maza, ka kuma sa musu taguwoyi. 15Sa'an nan ka shafa musu mai kamar yadda ka shafa wa mahaifinsu domin su yi mini aiki a matsayin firistoci. Shafa musu man zai sa su zama firistoci din din din dukan zamanansu.”
16Haka kuwa Musa ya yi dukan abin da Ubangiji ya umarce shi. 17A rana ta fari ga wata na fari a shekara ta biyu, aka kafa alfarwa. 18Sai musa ya kafa alfarwa, ya kafa kwasfanta, ya jera katakanta, ya sa mata sandunanta, ya kakkafa dirkokinta. 19Sa'an nan ya shimfiɗa murfi a bisa alfarwa ya rufe alfarwar kamar yadda Ubangiji ya umarce shi. 20Sai ya ɗauki dokoki goma ɗin, ya sa a akwatin, ya kuma zura sandunan a ƙawanen akwatin, sa'an nan ya sa murfin a bisansa. 21Ya kawo akwatin a cikin alfarwa, sa'an nan ya sa labulen don kāre akwatin alkawari, kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.
22Musa ya sa teburin cikin alfarwa ta sujada, a wajen gefen arewa na alfarwa, a gaban labulen. 23Sa'an nan ya jera gurasa daki-daki a bisa teburin a gaban Ubangiji, kamar yadda Ubangiji ya umarce shi. 24Ya kuma sa alkukin a cikin alfarwa ta sujada daura da teburin a wajen gefen kudu na alfarwa. 25Ya kunna fitilun a gaban Ubangiji, kamar yadda Ubangiji ya umarce shi. 26Ya kuma sa bagade na zinariya a cikin alfarwa ta sujada daga gaban labulen. 27Sai ya ƙona turare mai ƙanshi a bisansa kamar yadda Ubangiji ya umarce shi. 28Ya sa labule a ƙofar alfarwa. 29Ya kuma sa bagade na ƙona hadaya a ƙofar alfarwa ta sujada, sa'an nan ya miƙa hadaya ta ƙonawa da ta gari kamar yadda Ubangiji ya umarce shi. 30Ya kuma sa daro a tsakanin alfarwa ta sujada da bagaden, sa'an nan ya zuba ruwa a ciki don wanka. 31A cikinsa Musa da Haruna da 'ya'yansa maza sukan wanke hannuwansu da ƙafafunsu, 32sa'ad da suke shiga cikin alfarwa ta sujada, da sa'ad da sukan kusaci bagaden kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa. 33Ya kuma yi farfajiya kewaye da alfarwa da bagaden, ya sa labulen ƙofar farfajiyar. Da haka Musa ya gama aikin.
Saukowar Girgije a bisa Alfarwa ta Sujada
34 # 1Sar 8.10,11; Ish 6.4; Eze 43.4,5; W.Yah 15.8 Sa'an nan girgije ya rufe alfarwa ta sujada, ɗaukakar Ubangiji kuma ta cika alfarwa. 35Musa kuwa bai iya shiga alfarwa ta sujada ba domin girgijen yana zaune a bisanta, ɗaukakar Ubangiji kuma ta cika alfarwa. 36Cikin tafiyar Isra'ilawa duka, sukan kama tafiyarsu ne a duk sa'ad da girgijen ya tashi daga kan alfarwa. 37Idan girgijen bai tashi ba, su kuma ba za su tashi ba, sai a ranar da ya tashi. 38Gama a cikin tafiyarsu duka, girgijen Ubangiji yana kan alfarwa da rana, da dare kuwa wuta yake cikinsa domin dukan Isra'ilawa su gani.

Currently Selected:

Fit 40: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in

YouVersion uses cookies to personalize your experience. By using our website, you accept our use of cookies as described in our Privacy Policy