YouVersion Logo
Search Icon

Fit 38

38
Bagaden Ƙona Hadaya
(Fit 27.1-8)
1Ya kuma yi bagaden ƙona hadaya da itacen ƙirya, tsawonsa kamu biyar, fāɗinsa kamu biyar, murabba'i ke nan, tsayinsa kuwa kamu uku. 2Ya yi masa zankaye a kusurwoyinsa huɗu. Zankayen a haɗe suke da shi. Ya dalaye bagaden da tagulla. 3Da tagulla ya yi duk kayayyakin bagaden, da kwanoni, da babban cokali, da daruna, da cokula masu yatsotsi, da farantan wuta. 4Ya yi wa bagaden raga da tagulla, ya sa ta a tsakiya. 5Ya sa ƙawane huɗu a kusurwoyi huɗu na ragar tagulla don zura sanduna. 6Ya kuma yi sanduna da itacen ƙirya, ya dalaye su da tagulla. 7Sai ya zura sandunan cikin ƙawane na gyaffan bagaden don ɗaukarsa. Ya yi bagaden da itace sa'an nan ya robe cikinsa.
Yin Daron Wanka
(Fit 30.18)
8 # Fit 30.18 Ya yi daron wanka da tagulla, da gammonsa na tagulla, daga madubai na mata masu yin aiki a ƙofar alfarwa ta sujada.
Farfajiyar Alfarwa ta Sujada
(Fit 27.9-19)
9Ya kuma yi farfajiya. Ya yi labulenta na gefen kudu da lallausan zaren lilin, tsawonsu kamu ɗari ne. 10Da tagulla aka yi dirkokinsa ashirin, da kwasfan dirkoki guda ashirin, amma da azurfa aka yi maratayan dirkoki da maɗaurai. 11Tsawon labule na wajen gefen arewa kamu ɗari ne. An yi dirkokinsa guda ashirin da kwasfansu ashirin da tagulla, amma an yi maratayan dirkoki da maɗaurai da azurfa. 12Labule na gefen yamma kamu hamsin ne, dirkokinsa kuwa guda goma ne, da kwasfansu guda goma. An yi maratayan dirkoki, da maɗaurai da azurfa. 13Tsawon gefen gabas kamu hamsin ne. 14Labule na gefe ɗaya na ƙofar, kamu goma sha biyar ne, da dirkokinsu guda uku da kwasfan dirkoki guda uku. 15Akwai kuma labule mai kamu goma sha biyar a gefe biyu na ƙofar farfajiyar. Labulen yana da dirkoki guda uku da kwasfan dirkoki guda uku. 16Duk labulen da yake kewaye da farfajiya an yi shi da lallausan zaren lilin. 17An yi kwasfan dirkoki duka da tagulla, amma maratayan dirkoki da maɗauransu an yi su da azurfa. An dalaye kawunansu da azurfa. Dirkokin farfajiya duka suna da maɗaurai na azurfa. 18An yi wa labulen ƙofar farfajiya ado na ɗinki da na shuɗi, da na shunayya, da na mulufi, da na lallausan zaren lilin. Tsawonsa kamu ashirin, tsayinsa kamu biyar daidai da labulen farfajiya. 19An yi dirkokin labulen guda huɗu, da kwasfan dirkoki guda huɗu da tagulla, amma da azurfa aka yi maratayan dirkokin. An dalaye kawunansu da maɗauransu da azurfa. 20An yi turakun alfarwa ta sujada da na farfajiya duka da tagulla.
Ƙarafan da aka yi Amfani da Su
21Wannan shi ne lissafin abubuwan da aka yi alfarwa ta sujada da su, yadda aka lasafta bisa ga umarnin Musa domin aikin Lawiyawa a ƙarƙashin jagorar Itamar, ɗan Haruna firist.
22Sai Bezalel ɗan Uri, ɗan Hur, na kabilar Yahuza, ya yi dukan abin da Ubangiji ya umarci Musa. 23Tare da shi kuma ga Oholiyab ɗan Ahisamak na kabilar Dan, gwani ne cikin aikin zāne-zāne, da ɗinki na shuɗi, da na shunayya, da na mulufi, da na lallausan zaren lilin.
24Dukan zinariya da aka yi aikace-aikacen da ita na alfarwa ta sujada sadaka ce talanti ashirin da tara ne da shekel ɗari bakwai da talatin bisa ga ma'aunin kuɗin da ake aiki da shi. 25#Fit 30.11-16 Azurfar da aka samu daga ƙidayar taron jama'a talanti ɗari ne, da shekel dubu ɗaya da ɗari bakwai da saba'in da biyar (1,775) bisa ga ma'aunin kuɗin da ake aiki da shi. 26#Mat 17.24 Kowane mutum da aka ƙidaya ya ba da rabin shekel. Duk mai shekara ashirin ko fi an ƙidaya shi, aka sami maza dubu ɗari shida da dubu uku da ɗari biyar da hamsin (603,550). 27An mori azurfa talanti ɗari don yin kwasfa na alfarwa, da kwasfa na labule. An yi kwasfa ɗari da azurfa talanti ɗari, wato kwasfa ɗaya talanti ɗaya ke nan. 28An yi maratayan dirkoki da azurfa shekel dubu ɗaya da ɗari bakwai da saba'in da biyar (1,775), sa'an nan an dalaye kawunansu, an kuma yi musu maɗaurai. 29Tagullar da aka bayar kuwa, talanti saba'in da shekel dubu biyu da ɗari huɗu (2,400). 30Da tagullar ce ya yi kwasfan ƙofar alfarwa ta sujada, da bagade, da ragarsa, da dukan kayayyakin bagaden. 31Da tagullar kuma aka yi kwasfan farfajiya, da kwasfan ƙofar farfajiya, da dukan turakun alfarwar da na farfajiyar.

Currently Selected:

Fit 38: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in

YouVersion uses cookies to personalize your experience. By using our website, you accept our use of cookies as described in our Privacy Policy