YouVersion Logo
Search Icon

M.Had 6

6
Rashin Ma'anar Rai
1Na kuma lura, a duniyan nan an yi wa ɗan adam rashin adalci ƙwarai. 2Allah yakan ba wani mutum dukiya, da daraja, da wadata, i, da kowane abu da yake bukata. Amma bai ba shi iko ya more su ba. A maimakonsa wani baƙo ne zai more su. Wannan aikin banza ne ba kuwa daidai ba ne. 3Mai yiwuwa ne mutum ya haifi 'ya'ya ɗari ya kuma yi tsawon rai, amma kome tsawon ransa ba wani abu ba ne idan ba shi da farin ciki, bai kuma sami kyakkyawar binnewa ba. Sai na ce, gara jaririn da aka haifa matacce da shi. 4Haihuwar ba ta amfane shi kome ba, gama ya zo daga duhu ya koma duhu inda aka manta da shi. 5-6Gama bai taɓa ganin hasken rana ba, bai kuma san abin da ake ce da shi rai ba. Amma duk da haka ya dai huta, fiye da mutumin da bai more wa rai ba, ko da ya shekara dubu biyu. Duk da haka dukansu wuri ɗaya za su tafi.
7Dukan wahalar da ɗan adam yake yi ta samun abinci ce, amma duk da haka bai taɓa ƙoshi ba. 8Da me mai hikima ya fi wawa? Wace riba ce kuma matalaucin da ya iya zama da mutane zai samu? 9Abin da ya zo hannu ya fi dogon buri gama dogon buri aikin banza ne, harbin iska kawai.
10Kowane abu da ya kasance, an riga an ba shi suna, yadda aka yi mutum haka zai zama. Ba kuwa zai iya gardama da abin da ya fi ƙarfinsa ba. 11Yawan magana yakan ɓata al'amari. Wane amfani zai yi wa mutum? 12Wa ya san abin da ya fi dacewa ga mutum a 'yan kwanakinsa marasa amfani? Sukan wuce kamar inuwa. Wa kuma zai iya faɗa wa mutum abin da zai faru a duniya bayan rasuwarsa?

Currently Selected:

M.Had 6: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in