M.Had 7
7
Fifikon Hikima
1 #
K.Mag 22.1
Kyakkyawan suna ya fi man ƙanshi tsada, ranar mutuwa kuma ta fi ranar haihuwa.
2Gara a tafi gidan da ake makoki
Da a tafi gidan da ake biki,
Gama wannan shi ne ƙarshen dukan mutane.
Ya kamata duk mai rai ya riƙe wannan a zuciyarsa,
Mutuwa tana jiran kowa.
3Baƙin ciki ya fi dariya,
Gama baƙin ciki yakan kawo gyara.
4Mai hikima yakan yi tunanin mutuwa,
Amma wawa yakan yi tunanin shagalin duniya.
5Gara mutum ya ji tsautawar mai hikima,
Da ya ji wawaye suna yabonsa.
6Dariyar wawa kamar ƙarar ƙayar da take karce gindin tukunya ce.
Wannan ma aikin banza ne.
7Hakika zalunci yakan sa mai hikima ya zama wawa,
Karɓar rashawa kuma yakan lalata hali.
8Gara ƙarshen abu da farkonsa.
Mai haƙuri kuma ya fi mai girmankai.
9 #
Yak 1.19
Ka kame fushinka,
Gama wawa ne yake cike da fushi.
10Kada ka yi tambaya, cewa me ya sa zamanan dā suka fi na yanzu?
Gama wannan tambaya ba ta hikima ba ce.
11Ya kamata kowane mutum ya zama mai hikima,
Gama tana da kyau kamar cin gādo.
12Hikima mafaka ce, takan kāre mutum kamar yadda kuɗi yake yi.
Kiyayewar da hikima takan yi wa mai ita, ita ce amfanin ilimi.
13Ka yi tunanin aikin Allah,
Wa ya isa ya miƙe abin da ya tanƙware?
14In kana jin daɗi, ka yi murna,
In kuma wahala kake sha, ka tuna,
Allah ne ya yi duka biyunsa,
Don kada mutum ya san abin da zai faru a nan gaba.
15A kwanakina marasa amfani na ga kowane irin abu. Adali ba safai yakan yi tsawon rai ba, mugu kuwa yakan yi tsawon rai a mugayen ayyukansa. 16Kada ka cika yin adalci, kada kuma ka cika yin hikima, gama don me za ka kashe kanka? 17Kada ka cika yin mugunta, kada kuma ka cika yin wauta, gama don me za ka mutu tun kwanakinka ba su cika ba? 18Idan ka riƙe wannan zai amfane ka. Kada ka bar wancan, gama shi wanda yake tsoron Allah zai yi amfani da su.
19Abin da hikima take iya yi wa mutum ɗaya ya fi abin da masu mulki goma za su yi wa birni.
20Ba wani mutum a duniyan nan wanda yake aikata abin da yake daidai dukan lokaci, ba tare da yin kuskure ba.
21Kada ka kula da kowane abu da mutane suke faɗa, mai yiwuwa ne ka ji baranka yana zaginka. 22Kai kanka ka sani sau da yawa kakan zagi waɗansu mutane.
Neman Hikima
23Na yi amfani da hikimata don in jarraba wannan duka, domin na ɗaura aniya in zama mai hikima, amma abin ya fi ƙarfina. 24Wane ne zai iya sanin gaibi? Abin ya yi mana zurfi ƙwarai, yana da wuyar ganewa. 25Amma na duƙufa neman ilimi, ina ta yin nazari, ina nema in san hikima da amsoshin tambayoyina, in kuma san mugunta da wautar dakikanci.
26Sai na iske wani abu da ya fi mutuwa ɗaci, wato mace wadda ƙaunar da take yi maka za ta kama ka kamar tarko, kamar kuma raga. Rungumewar da za ta yi maka za ta ɗaure ka kamar sarƙa. Wanda Allah yake jin daɗinsa zai tsere mata, amma za ta kama mai zunubi. 27Haka ne, in ji Mai Hadishi, da kaɗan da kaɗan na gane wannan sa'ad da nake neman amsa. 28Amsar da nake nema ban samu ba. Na sami mutum ɗaya mai hikima, wato a cikin mutum dubu, amma daga cikin mata ban sami ko ɗaya ba. 29Wannan ne kaɗai abin da na gane, tsaf Allah ya yi mu, amma mu muka rikitar da kanmu.
Currently Selected:
M.Had 7: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979