M.Had 5
5
Kada ka Yi Gaggawar Yin Wa'adi
1Ka yi hankali lokacin da kake shiga Haikali. Gara ka tafi can da niyyar koyon wani abu, da ka miƙa hadaya kamar waɗansu wawaye da ba su san halal da haram ba. 2Yi tunani kafin ka yi magana, kada ka yi wa Allah wa'adi na gaggawa. Allah yana Sama kai kuwa kana duniya. Don haka kada ka faɗa fiye da abin da ya kamata. 3Yawan damuwarka yana iya sa ka yi mafarkai. Yawan maganarka kuma yana iya sa ka ka yi maganar wauta. 4#Zab 66.13,14 Sa'ad da ka yi wa'adi ga Allah, yi hanzari ka cika, gama wawa ba shi da wani amfani a gare shi. Sai ka cika wa'adin da ka yi! 5Gara kada ka yi wa'adi, da ka yi wa'adi, amma ba ka cika ba. 6Kada ka bar maganar bakinka ta kai ka ga yin zunubi, har ka ce wa manzon Allah, ba haka kake nufi ba. Don me za ka sa Allah ya yi fushi da kai, har ya hallakar da abin da ka yi wahalarsa? 7Yawan mafarkanka, da dukan ayyukanka, da yawan maganganunka duk banza ne, duk da haka ya fi maka amfani ka yi tsoron Allah.
Rai Banza Ne
8Idan ka ga hukuma na zaluntar talakawa, ba ta yi musu adalci, ba ta kiyaye hakkinsu, kada ka yi mamaki. Kowane shugaba yana da shugaban da yake goyon bayansa. Dukansu biyu suna da goyon bayan manyan shugabanni.
9Abin da ƙasa take bukata, shi ne sarkin da yake kulawa da aikin gona.
10Idan kana ƙaunar kuɗi, daɗi ba zai ishe ka ba, wanda kuma yake ƙaunar dukiya, ba zai ƙoshi da riba ba, wannan kuma aikin banza ne. 11Gwargwadon dukiyarka gwargwadon mutanen da za ka ciyar, ribarka kaɗai ita ce sanin kana da dukiya. 12Ma'aikaci, ko yana da isasshen abinci, ko ba shi da isasshe, duk da haka yakan ji daɗin barcinsa da dare. Amma mawadaci yakan kwana bai rintsa ba, saboda yawan tunani.
13Wani mugun abu da na gani a duniyan nan, shi ne mutane sun ajiye kuɗi domin lokacin da za su bukace su. 14Amma sukan lalace saboda muguwar ma'amala, har ba abin da ya ragu da za su bar wa 'ya'yansu gado. 15#Ayu 1.21; Zab 49.17; 1Tim 6.7 Mukan bar duniyan nan kamar yadda muka shigo ta, ba mu da kome. Dukan ayyukanmu, ba abin da za mu ɗauka mu tafi da shi. 16Wannan mugun abu ne, mukan tafi kamar yadda muka zo. Mukan yi aiki, muna ƙoƙari mu kama iska, me muka samu ke nan? 17Mun yi zamanmu a duhu, da baƙin ciki, da damuwa, da fushi, da cuta.
18Ga abin da na gani yana da kyau, ya kuma dace, shi ne kurum mutum ya ci, ya sha, ya ji daɗin aikin da ya yi a 'yan kwanakin rai da Allah ya ba shi, gama wannan shi aka ƙaddara wa mutum. 19Duk wanda Allah ya ba wadata da dukiya ya kuma bar shi ya ci moriyarsu, sai ya yi godiya ya ci moriyar aikin da ya yi, wannan kyauta ce ta Allah. 20Tun da yake Allah ya yarje masa, ya zauna da farin ciki, ba ya cika damuwa saboda rashin tsawon kwanaki.
Currently Selected:
M.Had 5: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979