YouVersion Logo
Search Icon

M.Had 4

4
1Sa'an nan na sāke dubawa a kan rashin adalcin da yake ci gaba a duniyan nan. Waɗanda ake zalunta suna kuka, ba kuwa wanda zai taimake su, domin waɗanda suke zaluntarsu suke da iko. 2Ina ƙyashin waɗanda suka mutu, gama sun fi waɗanda suke da rai yanzu jin daɗi. 3Amma wanda ya fi su jin daɗi duka, shi ne wanda bai taɓa rayuwa ba, balle ya ga rashin adalcin da yake ta ci gaba a duniyan nan.
4Na gane dalilin da ya sa mutane suke aiki ƙwarai don su ci nasara, so suke su fi kowa samu. Wannan ma aikin banza ne harbin iska kawai. 5Za su ce, “Wawa ne zai ƙi yin aiki, ya zauna har yunwa ta kashe shi.” 6Gara tafin hannu guda cike da kwanciyar rai, da tafin hannu biyu cike da tashin hankali, harbin iska ne kawai.
7Na kuma ga wani abu a zaman mutum, wanda bai amfana kome ba, 8mutumin da ba shi da kowa, ba ɗa, ba ɗan'uwa, duk da haka a kullum yana ta fama da aiki. Bai taɓa ƙoshi da wadatar da yake da ita ba. Saboda me yana ta fama da aiki, ya hana wa kansa jin daɗi? Wannan ma aikin banza ne, zaman baƙin cikin ne.
9Biyu sun fi ɗaya, gama za su fi samun amfanin wahalar aikinsu. 10Gama idan ɗaya daga cikinsu ya fāɗi, ɗayan zai taimake shi ya tashi, amma idan ya faɗi yana shi kaɗai, to, tir, domin ba wanda zai taimake shi. 11Idan mutum biyu sun kwanta tare, za su ji ɗumin juna, amma ƙaƙa mutum ɗaya zai ji ɗumi? 12Mutum biyu za su iya kāre kansu su ci nasara, amma mutum ɗaya ba zai iya kāre kansa ya ci nasara a kan wanda ya kawo masa hari ba. Igiya riɓi uku tana da wuyar tsinkawa.
13-14Mutum yana iya tashi daga matsayin talauci ya zama sarki a ƙasarsa, ko ya fita daga kurkuku ya hau gadon sarauta. Amma lokacin da sarki ya tsufa, idan wautarsa ta hana shi karɓar shawara, bai fi saurayin ɗin da yake talaka mai basira ba. 15Na yi tunani a kan dukan mutanen da suke zaune a duniyan nan, sai na gane a cikinsu akwai saurayin da zai maye matsayin sarkin. 16Mutanen da sarki yake mallaka suna da yawan gaske. Amma bayan ba shi ba wanda zai gode masa saboda ayyukan da ya yi. Hakika wannan ma aikin banza ne, harbin iska kawai.

Currently Selected:

M.Had 4: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in