1
M.Had 5:2
Littafi Mai Tsarki
HAU
Yi tunani kafin ka yi magana, kada ka yi wa Allah wa'adi na gaggawa. Allah yana Sama kai kuwa kana duniya. Don haka kada ka faɗa fiye da abin da ya kamata.
Compare
Explore M.Had 5:2
2
M.Had 5:19
Duk wanda Allah ya ba wadata da dukiya ya kuma bar shi ya ci moriyarsu, sai ya yi godiya ya ci moriyar aikin da ya yi, wannan kyauta ce ta Allah.
Explore M.Had 5:19
3
M.Had 5:10
Idan kana ƙaunar kuɗi, daɗi ba zai ishe ka ba, wanda kuma yake ƙaunar dukiya, ba zai ƙoshi da riba ba, wannan kuma aikin banza ne.
Explore M.Had 5:10
4
M.Had 5:1
Ka yi hankali lokacin da kake shiga Haikali. Gara ka tafi can da niyyar koyon wani abu, da ka miƙa hadaya kamar waɗansu wawaye da ba su san halal da haram ba.
Explore M.Had 5:1
5
M.Had 5:4
Sa'ad da ka yi wa'adi ga Allah, yi hanzari ka cika, gama wawa ba shi da wani amfani a gare shi. Sai ka cika wa'adin da ka yi!
Explore M.Had 5:4
6
M.Had 5:5
Gara kada ka yi wa'adi, da ka yi wa'adi, amma ba ka cika ba.
Explore M.Had 5:5
7
M.Had 5:12
Ma'aikaci, ko yana da isasshen abinci, ko ba shi da isasshe, duk da haka yakan ji daɗin barcinsa da dare. Amma mawadaci yakan kwana bai rintsa ba, saboda yawan tunani.
Explore M.Had 5:12
8
M.Had 5:15
Mukan bar duniyan nan kamar yadda muka shigo ta, ba mu da kome. Dukan ayyukanmu, ba abin da za mu ɗauka mu tafi da shi.
Explore M.Had 5:15
Home
Bible
Plans
Videos