M.Had 10
10
Sakamakon Wauta
1Matattun ƙudaje sukan sa man ƙanshi ya yi wari, haka nan wauta kaɗan takan ɓata hikima da daraja.
2Zuciyar mai hikima takan kai shi ga yin abin da yake daidai, amma zuciyar wawa takan kai shi ga yin mugun abu. 3Ko lokacin da wawa yake tafiya a hanya, yakan nuna ba shi da hankali, yakan kuma bayyana wa kowa shi wawa ne.
4Idan mai mulki ya husata da kai, kada ka bar inda kake, gama kwantar da hankali yakan sa a yafe manyan laifofi.
5Akwai mugunta wadda na gani a duniya, wato kuskuren da masu mulki suke yi. 6Ana ba wawaye manyan matsayi, attajirai kuwa ana ƙasƙantar da su. 7Na taɓa ganin bayi a kan dawakai, shugabanni kuwa suna tafiya a ƙasa kamar bayi.
8 #
Zab 7.15; K.Mag 26.27 Wanda ya haƙa rami shi ne zai fāɗa a ciki. Wanda kuma ya rushe katanga, shi maciji zai sara. 9Wanda yake farfasa duwatsu shi za su yi wa rauni. Wanda kuma yake faskare itace yana cikin hatsarinsu. 10Idan gatari ya dakushe ba a wasa shi ba, dole ne a yi amfani da ƙarfi da yawa, amma hikima takan taimake shi ya ci nasara. 11Idan maciji ya sari mutum kafin a ba shi makarin gardi kuma, ba shi da wani amfani. 12Maganar mai hikima alheri ce, amma maganganun wawa za su hallaka shi. 13Farkon maganganunsa wauta ne, ƙarshensu kuma mugunta ne da hauka. 14Wawa ya cika yawan surutu.
Wa ya san abin da zai faru nan gaba? Wa zai iya faɗa masa abin da zai faru bayan rasuwarsa?
15Wahalar wawa takan gajiyar da shi, har bai san hanyar zuwa gari ba.
16Kaitonki, ya ƙasa wadda sarkinki yaro ne, shugabanninki kuma suna ta shagalinsu tun da safe. 17Mai farin ciki ce, ke ƙasar da sarkinki mai dattako ne, shugabanninki kuma suka ci a kan kari don su sami ƙarfi, ba domin su bugu ba.
18Saboda lalaci ɗaki yakan yi yoyo, sai tsaiko ya lotsa.
19Akan shirya abinci don jin daɗi, ruwan inabi kuwa don faranta zuciya, amma ba za ka sami ko ɗaya ba, sai idan kana da kuɗi.
20Kada ka zagi sarki ko a cikin zuciyarka, kada kuma ka zagi mawadaci a cikin ɗakin kwananka, gama tsuntsu zai kai maganarka, wani taliki mai fikafikai zai tone asirinka.
Currently Selected:
M.Had 10: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979