YouVersion Logo
Search Icon

M.Had 11

11
Abin da Mai Hikima Yakan Yi
1Ka jefa kyautarka a baya, ka tsince ta a gaba. 2Ka raba abin da yake hannunka ga mutum bakwai ko takwas, gama ba ka san irin masifar da za ta auka wa duniya ba.
3Idan gizagizai sun cika da ruwa sukan sheƙar da shi ƙasa. A inda itace ya faɗi, a nan zai kwanta, ko wajen kudu ko arewa. 4Wanda yake la'akari da iska, ba zai yi shuka ba, wanda kuma yake la'akari da gizagizai, ba zai yi girbi ba. 5Kamar yadda ba ka san hanyar iska ba, ko yadda ƙasusuwan jariri suke girma a mahaifar uwarsa, haka nan kuma ba ka san aikin Allah ba, wato wanda ya yi abu duka. 6Ka shuka iri da safe, da yamma kuma kada ka janye hannunka, gama ba ka san wanda zai yi albarka ba, ko wannan ko wancan, ko kuma duka biyunsu su yi albarka.
7Haske yana da daɗi, abu mai kyau kuma idanu su dubi hasken rana. 8Idan mutum ya rayu har shekaru da yawa, bari ya yi murna a cikinsu duka. Sai dai kuma ya tuna da kwanakin duhu, gama sun fi yawa. Duk abin da ya faru banza ne.
Shawara ga Matasa
9Ya saurayi! Ka yi murna a lokacin ƙuruciyarka, ka bar zuciyarka ta yi farin ciki a kwanakin samartakarka. Ka bi nufin zuciyarka da sha'awar idanunka. Amma ka sani fa, a cikin al'amuran nan duka Allah zai shara'anta ka.
10Kada ka bar kome ya dame ka, ko ya yi maka zafi a rai, gama ƙuruciya da samartaka ba za su dawwama ba.

Currently Selected:

M.Had 11: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in