YouVersion Logo
Search Icon

M.Had 9

9
Rashin Daidaitawa
1Na daɗe ina tunani ƙwarai a kan wannan abu duka, yadda Allah yake sarrafa ayyukan masu hikima da na adalai, har da ƙaunarsu da ƙiyayyarsu. Ba wanda ya san abin da zai faru nan gaba. 2Ba wani bambanci. Makoma ɗaya ce, ta adali da ta mugu, da ta mutumin kirki da ta marar kirki, da ta tsattsarka da ta marar tsarki, da ta masu yin sujada da ta marasa yi. Mutumin kirki bai fi mai zunubi ba. Wanda ya yi rantsuwa bai fi wanda bai yi ba. 3Duk makomarsu ɗaya ce, wannan ita ce ɓarnar da take faruwa a duniya. Muddin mutane suna da rai tunaninsu cike yake da mugunta da rashin hankali. Bayan haka sukan mutu. 4Amma dukan wanda yake da rai a wannan duniya ta rayayyu, yana sa zuciya, gara rayayyen kare da mataccen zaki. 5Hakika rayayyu sun san za su mutu, amma matattu ba su san kome ba. Ba su da wani sauran lada nan gaba, an manta da su ke nan sam. 6Ƙaunarsu, da ƙiyayyarsu, da kishinsu sun mutu tare da su. Ba za su ƙara yin wani abu da ake yi a duniya ba.
7Yi tafiyarka, ka ci abincinka da farin ciki, ka sha ruwan inabinka da fara'a, gama abin da ka yi duka daidai ne a wurin Allah. 8Ka yi farin ciki da fara'a kullum. 9Ka yi nishaɗi da matar da kake ƙauna, dukan kwanakin ranka na banza waɗanda Allah ya ba ka a wannan duniya, ka more kowace rana, wannan ne kaɗai rabonka na wahalar aikinka a duniya. 10Duk abin da kake iya yi, ka yi shi da iyakar iyawarka, domin ba aiki, ko tunani, ko ilimi, ko hikima a lahira, gama can za ka.
11Na gane wani abu kuma, ashe, a duniyan nan ba kullum maguji ne yake cin tsere ba, ba kullum jarumi ne yake cin nasara ba. Ba kullum mai hikima ne da abinci ba, ba kullum mai basira ne yake da wadata ba, ba kullum gwani ne yake samun tagomashi ba. Amma sa'a, da tsautsayi, sukan sami kowannensu. 12Gama mutum bai san lokacinsa ba, kamar kifayen da akan kama da taru, kamar kuma tsuntsayen da akan kama da tarko, haka nan mugun lokaci yakan auko wa 'yan adam farat ɗaya.
Hikima ta Fi Iko
13A duniyar nan na ga wani babban al'amari game da hikima. 14Dā akwai wani ɗan ƙaramin gari, mutane kuma suke ciki. Sai wani babban sarki ya kawo masa yaƙi, ya kafa masa babban sansani. 15Akwai wani matalauci, mai hikima, a garin, sai ya ceci garin ta wurin hikimarsa. Duk da haka ba wanda ya tuna da wannan matalauci. 16Na ce hikima ta fi ƙarfe ƙarfi, ko da yake an raina hikimar matalauci da maganarsa. 17Gara a kasa kunne ga tattausar maganar mai hikima, da a kasa kunne ga hargagin mai mulki a tsakanin wawaye. 18Hikima ta fi makaman yaƙi, amma mai zunubi ɗaya yakan yi ɓarna mai yawa.

Currently Selected:

M.Had 9: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in