YouVersion Logo
Search Icon

1Yah 3

3
'Ya'yan Allah
1 # Yah 1.12 Ku dubi irin ƙaunar da Uba ya nuna mana, har yake ce da mu 'ya'yan Allah, haka kuwa muke. Abin da ya sa duniya ba ta san mu ba, don ba ta san shi ba ne. 2Ya ku ƙaunatattuna, a yanzu mu 'ya'yan Allah ne, yadda za mu zama nan gaba kuwa, ba a bayyana ba tukuna, amma mun sani sa'ad da ya bayyana, za mu zama kamarsa, domin za mu gan shi kamar yadda yake. 3Duk mai ƙwallafa sa zuciya gare shi haka, yana tsarkake kansa ke nan, kamar yadda shi yake Mai Tsarki.
4Duk mai aikata zunubi ya yi tawaye ke nan. Zunubi tawaye ne. 5#Yah 1.29 Kun dai sani an bayyana shi domin yă ɗauke zunubai ne, a gare shi kuma ba zunubi. 6Kowa da yake a zaune a cikinsa, ba ya aikata zunubi. Kowa da yake aikata zunubi, bai taɓa ganinsa ba, bai ma san shi ba. 7Ya ku 'ya'yana ƙanana, kada fa kowa ya ɓad da ku. Shi wanda yake aikata adalci, mai adalci ne, kamar yadda Almasihu mai adalci ne. 8Duk mai aikata zunubi, na Iblis ne, don tun farko Iblis mai aikata zunubi ne. Dalilin bayyanar Ɗan Allah shi ne domin yă rushe aikin Iblis. 9Duk wanda yake haifaffen Allah, ba yakan aikata zunubi ba, domin irinsa yana a cikinsa a zaune, ba yakan aikata zunubi ba, da yake shi haifaffen Allah ne. 10Ta haka sai a ga waɗanda suke 'ya'yan Allah, da kuma waɗanda suke 'ya'yan Iblis, wato duk wanda ba ya aikata adalci, ba na Allah ba ne, haka kuma wanda ba ya ƙaunar ɗan'uwansa.
Ku Ƙaunaci Juna
11 # Yah 13.34 Wannan shi ne jawabin da kuka ji tun farko, cewa dai mu ƙaunaci juna, 12#Far 4.8 kada mu zama kamar Kayinu, wanda yake na Mugun, har ma ya kashe ɗan'uwansa. To, don me ya kashe shi? Don ayyukansa mugaye ne, na ɗan'uwansa kuwa na kirki ne. 13Kada ku yi mamaki, 'yan'uwa, idan duniya take ƙinku. 14#Yah 5.24 Mu kam, mun sani mun riga mun tsere wa mutuwa, mun kai ga rai saboda muna ƙaunar 'yan'uwa. Wanda ba shi da ƙauna, zaman mutuwa yake yi. 15Kowa da yake ƙin dan'uwansa, mai kisankai ne. Ƙun kuwa sani ba mai kisankan da yake da rai madawwami a zauna tare da shi. 16Yadda muka san ƙauna ke nan, wato, ta wurin ba da ransa da ya yi saboda mu. Mu kuma ya kamata mu ba da ranmu saboda 'yan'uwa. 17Duk kuwa wanda yake da abin hannunsa, yake kuma ganin ɗan'uwansa da rashi, sa'an nan ya rufe ido gare shi, ƙaƙa ƙaunar Allah yake zaune a cikinsa? 18Ya ku 'ya'yana ƙanana, kada mu nuna ƙauna da fatar baki kawai, sai dai da aikatawa da kuma gaskiya.
Amincewa Gaban Allah
19Ta haka za mu tabbata mu na gaskiya ne, har kuma mu amince wa kanmu gaban Allah, 20duk sa'ad da zuciyarmu ta ba mu laifi, saboda Allah ya fi ta, ya kuma san kome. 21Ya ku ƙaunatattuna, in zuciyarmu ba ta ba mu laifi ba, sai mu je gaban Allah amincewa. 22Mukan kuma sami duk abin da muka roƙa a gare shi, domin muna bin umarninsa, muna kuma yin abin da yake so. 23#Yah 13.34; 15.12,17 Umarninsa kuwa shi ne mu gaskata da sunan Ɗansa Yesu Almasihu, mu kuma ƙaunaci juna, kamar yadda ya umarce mu. 24Duk mai bin umarnin Allah kuwa a dawwame yake cikinsa, Allah kuma a cikinsa. Ta haka muka tabbata ya dawwama a cikinmu, saboda Ruhun da ya ba mu.

Currently Selected:

1Yah 3: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in