YouVersion Logo
Search Icon

1Yah 4

4
Ruhun Allah da na Magabci
1Ya ku ƙaunatattuna, ba kowane ruhu za ku gaskata ba, sai dai ku jarraba ku gani ko na Allah ne, don annabawan ƙarya da yawa sun fito duniya. 2Ta haka za ku san Ruhun Allah, wato, duk ruhun da ya bayyana yarda, cewa Yesu Almasihu ya bayyana ne da jiki, shi ne na Allah. 3Duk ruhun kuwa da bai bayyana yarda ga Yesu ba, ba na Allah ba ne, wannan shi ne ruhun magabcin nan na Almasihu wanda kuka ji zai zo, a yanzu ma har yana duniya. 4Ya ku 'ya'yana ƙanana, ku kam na Allah ne, kun kuma ci nasara a kan waɗannan, domin shi wanda yake zuciyarku ya fi wanda yake duniya ƙarfi. 5Su kuwa na duniya ne, shi ya sa suke zance irin na duniya, duniya kuwa tana sauraronsu. 6Mu kam na Allah ne. Duk wanda ya san Allah yakan saurare mu, wanda yake ba na Allah ba kuwa, ba ya sauraronmu. Ta haka muka san Ruhu na gaskiya da ruhu na ƙarya.
Allah Ƙauna Ne
7Ya ku ƙaunatattuna, sai mu ƙaunaci juna, domin ƙauna ta Allah ce. Duk mai ƙauna kuwa haifaffen Allah ne, ya kuma san Allah. 8Wanda ba ya ƙauna, bai san Allah ba sam, domin Allah shi ne ƙauna. 9Ta haka aka bayyana ƙaunar Allah gare mu, da Allah ya aiko da Ɗansa makaɗaici a duniya, domin mu sami rai madawwami ta wurinsa. 10Ta haka ƙauna take, wato, ba mu ne muka ƙaunaci Allah ba, sai dai shi ne ya ƙaunace mu, ya aiko Ɗansa, hadayar sulhu saboda a gafarta zunubanmu. 11Ya ku ƙaunatattuna, tun da yake Allah ya ƙaunace mu haka, ai, mu ma ya kamata mu ƙaunaci juna. 12#Yah 1.18 Ba mutumin da ya taɓa ganin Allah daɗai, amma kuwa in muna ƙaunar juna sai Allah ya dawwama cikinmu, ƙaunar nan tasa kuma tă cika a cikinmu.
13Ta haka muka sani muna a zaune a cikinsa, shi kuma a cikinmu, saboda Ruhunsa da ya ba mu. 14Mun duba, muna kuma ba da shaida, cewa Uba ya aiko Ɗan ya zama Mai Ceton duniya. 15Kowa ya bayyana yarda, cewa Yesu Ɗan Allah ne, sai Allah yă dawwama a cikinsa, shi kuma a cikin Allah. 16Mun sani, mun kuma gaskata ƙaunar da Allah yake yi mana. Allah shi ne ƙauna wanda yake a dawwame cikin kauna kuwa, ya dawwama a cikin Allah ke nan, Allah kuma a cikinsa. 17Ta haka ne ƙauna ta cika a gare mu, har mu kasance da amincewa a ranar shari'a, domin kamar yadda yake, haka mu ma muke a duniyar nan. 18Ba tsoro ga ƙauna, amma cikakkiyar ƙauna takan yaye tsoro. Tsoro kansa ma azaba ne, mai jin tsoro kuwa ba shi da cikakkiyar ƙauna, 19Muna ƙauna, domin shi ne ya fara ƙaunarmu. 20Kowa ya ce yana ƙaunar Allah, alhali kuwa yana ƙin dan'uwansa, to, maƙaryaci ne. Don wanda ba ya ƙaunar ɗan'uwansa da yake gani, ba dama ya ƙaunaci Allah wanda bai taɓa gani ba. 21Wannan kuma shi ne umarnin da muka samu daga gare shi, cewa mai ƙaunar Allah, sai ya ƙaunaci ɗan'uwansa kuma.

Currently Selected:

1Yah 4: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in

YouVersion uses cookies to personalize your experience. By using our website, you accept our use of cookies as described in our Privacy Policy