1
1Yah 3:18
Littafi Mai Tsarki
HAU
Ya ku 'ya'yana ƙanana, kada mu nuna ƙauna da fatar baki kawai, sai dai da aikatawa da kuma gaskiya.
Compare
Explore 1Yah 3:18
2
1Yah 3:16
Yadda muka san ƙauna ke nan, wato, ta wurin ba da ransa da ya yi saboda mu. Mu kuma ya kamata mu ba da ranmu saboda 'yan'uwa.
Explore 1Yah 3:16
3
1Yah 3:1
Ku dubi irin ƙaunar da Uba ya nuna mana, har yake ce da mu 'ya'yan Allah, haka kuwa muke. Abin da ya sa duniya ba ta san mu ba, don ba ta san shi ba ne.
Explore 1Yah 3:1
4
1Yah 3:8
Duk mai aikata zunubi, na Iblis ne, don tun farko Iblis mai aikata zunubi ne. Dalilin bayyanar Ɗan Allah shi ne domin yă rushe aikin Iblis.
Explore 1Yah 3:8
5
1Yah 3:9
Duk wanda yake haifaffen Allah, ba yakan aikata zunubi ba, domin irinsa yana a cikinsa a zaune, ba yakan aikata zunubi ba, da yake shi haifaffen Allah ne.
Explore 1Yah 3:9
6
1Yah 3:17
Duk kuwa wanda yake da abin hannunsa, yake kuma ganin ɗan'uwansa da rashi, sa'an nan ya rufe ido gare shi, ƙaƙa ƙaunar Allah yake zaune a cikinsa?
Explore 1Yah 3:17
7
1Yah 3:24
Duk mai bin umarnin Allah kuwa a dawwame yake cikinsa, Allah kuma a cikinsa. Ta haka muka tabbata ya dawwama a cikinmu, saboda Ruhun da ya ba mu.
Explore 1Yah 3:24
8
1Yah 3:10
Ta haka sai a ga waɗanda suke 'ya'yan Allah, da kuma waɗanda suke 'ya'yan Iblis, wato duk wanda ba ya aikata adalci, ba na Allah ba ne, haka kuma wanda ba ya ƙaunar ɗan'uwansa.
Explore 1Yah 3:10
9
1Yah 3:11
Wannan shi ne jawabin da kuka ji tun farko, cewa dai mu ƙaunaci juna
Explore 1Yah 3:11
10
1Yah 3:13
Kada ku yi mamaki, 'yan'uwa, idan duniya take ƙinku.
Explore 1Yah 3:13