1Yah 2
2
Almasihu Mai Taimako Gun Allah
1Ya ku 'ya'yana ƙanana, ina rubuto muku wannan ne domin kada ku yi zunubi. In kuwa wani ya yi zunubi, muna da Mai Taimako a gun Uba, wato, Yesu Almasihu mai adalci. 2Shi kansa kuwa shi ne hadayar sulhu saboda gafarta zunubanmu, ba kuwa namu kaɗai ba, har ma na duniya duka. 3Ta haka za mu tabbata mun san shi, in dai muna bin umarninsa. 4Kowa ya ce ya san shi, ba ya kuwa bin umarninsa, maƙaryaci ne, gaskiya kuma ba ta tare da shi. 5Amma duk wanda yake kiyaye maganarsa, wannan kam, hakika yana ƙaunar Allah, cikakkiyar ƙauna. Ta haka muka tabbata muna cikinsa. 6Kowa ya ce yana zaune a cikinsa, ya kamata shi kansa ma ya yi irin zaman da shi ya yi.
Sabon Umarni
7 #
Yah 13.34
Ya ku ƙaunatattuna, ba fa wani sabon umarni nake rubuto muku ba, a'a, daɗaɗɗen umarnin nan ne wanda kuke da shi tun farko. Daɗaɗɗen umarnin nan kuwa, ai, shi ne maganar da kuka ji. 8Har wa yau sabon umarni nake rubuto muku, wanda yake tabbatacce ga Almasihu, da kuma gare ku, domin duhu yana shuɗewa, hakikanin haske kuma yana haskakawa. 9Kowa ya ce yana a cikin haske, yana kuwa ƙin ɗan'uwansa, ashe, a duhu yake har yanzu. 10Mai ƙaunar ɗan'uwansa, a haske yake zaune, ba kuma wani sanadin sa tuntuɓe a gare shi. 11Mai ƙin ɗan'uwansa kuwa, a duhu yake, a cikin duhu yake tafiya, bai san ma inda yake sa ƙafa ba, domin duhun ya makantar da shi.
12Ya ku 'ya'yana ƙanana, ina rubuto muku ne domin an gafarta muku zunubanku saboda sunansa. 13Ya ku dattawa, ina rubuto muku ne domin kun san shi, shi wanda yake tun fil'azal. Ya ku samari, ina rubuto muku ne domin kun ci nasara a kan Mugun nan. Ya ku 'yan yara, ina rubuto muku ne domin kun san Uba. 14Ya ku dattawa, na rubuto muku ne domin kun san shi, shi wanda yake tun fil'azal. Ya ku samari, na rubuto muku ne domin kuna da ƙarfi, Maganar Allah tana zauna a zuciyarku, kun kuma ci nasara a kan Mugun nan.
15Kada ku ƙaunaci duniya, ko abin da yake a cikinta. Kowa yake ƙaunar duniya, ba ya ƙaunar Uba ke nan sam. 16Don kuwa duk abin da yake duniya, kamar su sha'awa irin ta halin mutuntaka, da sha'awar ido, da kuma alfarmar banza, ba na Uba ba ne, na duniya ne. 17Duniyar kuwa tana shuɗewa da mugayen burinta, amma mai aikata nufin Allah zai dawwama har abada.
Magabcin Almasihu
18Ya ku 'yan yarana, zamanin ƙarshe ne fa. Kamar yadda kuka ji, magabcin Almasihu yana zuwa, ko a yanzu ma, magabtan Almasihu da yawa sun zo. Ta haka muka sani zamanin ƙarshe ne. 19Sun dai fita daga cikinmu, amma dā ma can ba namu ba ne. Don in da namu ne, da har yanzu suna tare da mu. Amma sun fita ne domin a bayyana dukansu ba namu a ciki. 20Ku kam, Mai Tsarkin nan ya shafe ku, dukanku kuma kun san gaskiya. 21Ina rubuto muku, ba don ba ku san gaskiya ba ne, a'a, sai domin kun san ta, kun kuma sani gaskiya ba ta haifar ƙarya. 22Wane ne maƙaryacin nan, in ba wanda ya mūsa Yesu shi ne Almasihu ba? Irin wannan shi ne magabcin Almasihu, shi wanda yake ƙin Uban da Ɗan. 23Ba mai ƙin Ɗan ya sami Uban. Kowa ya bayyana yarda ga Ɗan, ya sami Uban ke nan. 24Ku kam, abin da kuka ji tun da farko, sai ya zauna a zuciyarku. In abin da kuka ji tun farko ya zauna a zuciyarku, ku ma sai ku zauna cikin Ɗan, da kuma Uban. 25Wannan shi ne alkawarin da ya yi mana, wato, rai madawwami.
26Ina rubuto muku wannan ne a kan waɗanda suke ƙoƙarin ɓad da ku. 27Ku kam, shafar nan da kuka samu daga Ruhu Mai Tsarki tā tabbata a zuciyarku, ba sai wani ya koya muku ba. Amma kamar yadda shafar nan tasa take koya muku kome, ita kuwa gaskiya ce ba ƙarya ba, yadda dai ta koya muku, to, sai ku zauna a cikinsa.
28To a yanzu, ya ku 'ya'yana ƙanana, sai ku zauna cikinsa, domin sa'ad da ya bayyana, mu kasance da amincewa, kada kunya ta rufe mu a gabansa a ranar komowarsa. 29Da yake kun san shi mai adalci ne, ku dai tabbata duk mai aikata adalci haifaffensa ne.
Currently Selected:
1Yah 2: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979