Har da waɗanda suke yara ma, sukan ji kasala,
Samari sukan siƙe su fāɗi,
Amma waɗanda suke dogara ga Ubangiji domin taimako
Za su ji an sabunta ƙarfinsu.
Za su tashi da fikafikai kamar gaggafa,
Sa'ad da suke gudu, ba za su ji gajiya ba,
Sa'ad da suke tafiya, ba za su ji kasala ba.