Zan sa itatuwan al'ul su tsiro a hamada,
Da itacen ƙirya, da itacen ci-zaki, da zaitun.
Ƙeƙasasshiyar ƙasa za ta zama kurmi,
Jejin itatuwan fir.
Mutane za su ga wannan, su sani,
Ni Ubangiji, na yi shi.
Za su fahimta,
Allah Mai Tsarki na Isra'ila ya sa abin ya faru.”