Ish 40:6-7
Ish 40:6-7 HAU
Murya ta yi kira ta ce, “Ka yi shela!” Na yi tambaya na ce, “Shelar me zan yi?” “Ka yi shela, cewa dukan 'yan adam kamar ciyawa suke, Ba su fi furannin jeji tsawon rai ba. Ciyawa takan bushe, furanni kuma sukan yi yaushi Sa'ad da Ubangiji ya aiko da iska ta hura ta kansu. Mutane kuwa ba su fi ciyawa ƙarfi ba!





