Ish 40:12-14
Ish 40:12-14 HAU
Akwai wanda zai iya auna teku da tafin hannu, Ko sararin sama da tafin hannunsa? Akwai wanda zai iya tallabe turɓayar duniya a cikin finjali, Ko ya iya auna duwatsu da tuddai a ma'auni? Akwai wanda zai iya umartar Ubangiji ya yi abu? Wa zai iya koya wa Ubangiji, ko ya yi masa shawara? Da wa Allah yake yin shawara Domin ya sani, ya kuma fahimta, Ya kuma koyi yadda za a yi abubuwa?





