Zaf 2
2
Za a Hallaka Al'umman da Suke Kewaye da Su
1Ya ke al'umma marar kunya, ku tattaru, ku yi taro,
2Kafin a zartar da umarni,
Kafin a kore ku kamar ƙaiƙayi,
Kafin kuma zafin fushin Ubangiji ya auko muku,
Kafin ranar hasalar Ubangiji ta auko muku.
3Ku nemi Ubangiji,
Dukanku masu tawali'u na duniya,
Ku waɗanda kuke bin umarninsa.
Ku nemi adalci da tawali'u.
Watakila za a ɓoye ku a ranar hasalar Ubangiji.
4 #
Ish 14.29-31; Irm 47.1-7; Eze 25.15-17; Yow 3.4-8; Amos 1.6-8; Zak 9.5-7 Za a bar Gaza ba kowa,
Ashkelon za ta zama kufai,
Za a kori mutanen Ashdod da tsakar rana,
Ekron kuwa za a tumɓuke ta.
5Taku ta ƙare, ku mazaunan gaɓar teku, ke al'ummar Keretiyawa!
Ya Kan'ana, ƙasar Filistiyawa,
Maganar Ubangiji tana gāba da ke,
Za a hallaka ki har ba wanda zai ragu.
6Gāɓar teku za ta zama makiyaya, da wurin zaman masu kiwo,
Da kuma garakan tumaki.
7Gaɓar teku za ta zama ta mutanen Yahuza waɗanda suka ragu,
Wurin da za su yi kiwo.
Za su kwanta da maraice a gidajen Ashkelon,
Gama Ubangiji Allahnsu zai kula da su,
Zai kuwa mayar musu da albarkarsu ta dā.
8 #
Ish 15.1—16.14; 25.10-12; Irm 48.1-47; Eze 25.8-11; Amos 1.13-15;
Irm 49.1-6; Eze 21.28-32; 25.1-7; Amos 1.13-15 “Na ji ba'ar da Mowab ta yi, da zagin Ammonawa,
Yadda suka yi wa mutanena ba'a,
Sun yi alwashi, cewa za su cinye ƙasarsu.
9 #
Far 19.24
Domin haka, ni Ubangiji Mai Runduna Allah na Isra'ila,
Na rantse cewa,
Mowab za ta zama kamar Saduma,
Ammonawa kuma za su zama kamar Gwamrata.
Za su zama ƙasar ƙayayuwa
Da kwazazzaban gishiri marar amfani har abada.
Mutanena waɗanda suka ragu za su washe su, su mallake su.”
10Wannan shi ne hakkin girmankansu,
Saboda sun raina jama'ar Ubangiji Mai Runduna,
Sun yi musu alfarma.
11Ubangiji zai tsananta musu,
Zai kawo wa dukan gumakan da yake a duniya yunwa.
Kowane mutum a duniya zai yi masa sujada a inda yake,
Har da ƙasar sauran al'umma.
12 #
Ish 18.1-7
“Ku kuma, Habashawa, za a kashe ku da takobina.”
13 #
Ish 10.5-34; 14.24-27; Nah 1.1—3.19 Zai miƙa hannunsa gāba da arewa,
Zai hallaka Assuriya,
Zai mai da Nineba busasshen kufai
Marar amfani kamar hamada.
14Tumaki za su kwanta a tsakiyarta,
Da kuma kowace irin dabba ta kowace ƙasa.
Mujiya da bushiya za su zauna a kan ginshiƙanta,
Ga muryar kuka a taga.
Ga risɓewa a bakin ƙofa,
Gama za a kware rufin katakan itacen al'ul.
15Wannan shi ne birnin da yake da harka, mai zaman lafiya,
Wanda yake ce wa kansa, “Ba wani sai ni.”
Ga shi, ya zama kufai,
Wurin zaman dabbobi!
Duk wanda ya wuce ta wurin,
Zai yi tsaki, ya kaɗa kai.
Currently Selected:
Zaf 2: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979