YouVersion Logo
Search Icon

Zaf 1

1
Ranar Hasalar Ubangiji a kan Yahuza
1 # 2Sar 22.1—23.30; 2Tar 34.1—35.27 Ubangiji ya yi magana da Zafaniya ɗan Kushi, ɗan Gedaliya, ɗan Amariya, ɗan Hezekiya, a zamanin Yosiya ɗan Amon, Sarkin Yahuza.
2“Ni Ubangiji na ce, zan shafe dukan kome
Da yake a duniya.
3Zan shafe mutum da dabba,
Zan shafe tsuntsayen sararin sama da kifayen teku,
Zan kuma rushe gumakansu tare da mugaye,
Zan kuma datse ɗan adam daga duniya.
4“Zan miƙa hannuna gāba da Yahuza
Da dukan mazaunan Urushalima.
A wurin nan zan datse saura waɗanda suke bauta wa Ba'al,
Da kuma sunayen firistocin gumaka tare da firistocina,
5Da kuma waɗanda suke durƙusa wa rundunan sama a kan bene,
Waɗanda sukan durƙusa, su rantse da Ubangiji,
Duk da haka kuma sai su rantse da Milkom,
6Da kuma waɗanda suka juya, suka bar bin Ubangiji,
Waɗanda ba su neman Ubangiji, ba su kuma roƙonsa.”
7Ku yi tsit a gaban Ubangiji Allah!
Gama ranar Ubangiji ta gabato.
Ubangiji ya shirya ranar shari'a,
Ya kuma keɓe waɗanda za su aikata hukuncinsa.
8“A ranar shari'a, ni Ubangiji zan hukunta shugabanni da hakimai,
Da dukan waɗanda suke bin al'adun ƙasashen waje.
9A wannan rana zan hukunta duk wanda yake tsalle a bakin ƙofa,
Da waɗanda suke cika gidan maigidansu da zalunci da ha'inci.
10“Ni Ubangiji na ce, a wannan rana, za a ji kuka a Ƙofar Kifi,
Za a ji kururuwa kuma daga unguwa ta biyu,
Da amon ragargajewa daga kan tuddai.
11Ku yi kururuwa, ku mazaunan Maktesh,
Gama 'yan kasuwa sun ƙare,
An kuma datse dukan waɗanda suke awon azurfa.
12“A lokacin nan,
Zan bincike Urushalima da fitilu,
Zan kuwa hukunta marasa kulawa
Waɗanda suke zaman annashuwa,
Waɗanda suke cewa a zukatansu,
‘Ubangiji ba zai yi alheri ba,
Ba kuma zai yi mugunta ba!’
13Za a washe dukiyarsu,
Za a kuwa rurrushe gidajensu,
Ko da yake sun gina gidaje, ba za su zauna a ciki ba,
Ko da yake sun dasa inabi, ba za su sha ruwansa ba.”
14Babbar ranar Ubangiji ta gabato,
Tana gabatowa da sauri.
Ku ji muryar ranar Ubangiji!
Jarumi zai yi kuka mai zafi.
15Wannan rana ta hasala ce,
Ranar azaba da wahala,
Ranar lalatarwa da hallakarwa,
Ranar duhu baƙi ƙirin,
Ranar gizagizai da baƙin duhu,
16Ranar busar ƙaho da yin kururuwar yaƙi
Gāba da birane masu garu da hasumiyai masu tsawo.
17“Zan aukar wa mutane da wahala,
Za su kuwa yi tafiya kamar makafi,
Domin sun yi wa Ubangiji zunubi.
Za a zubar da jininsu kamar ƙura,
Namansu kuwa kamar taroso.”
18Azurfarsu da zinariyarsu ba za su cece su
A ranar hasalar Ubangiji ba,
A cikin zafin kishinsa
Dukan duniya za ta hallaka.
Zai kawo ƙarshen duniya duka nan da nan.

Currently Selected:

Zaf 1: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in