YouVersion Logo
Search Icon

Zaf 3

3
Zunubin Urushalima da Fansarta
1Taka ta ƙare, kai mai tayarwa,
Ƙazantaccen birni mai zalunci!
2Ba ya kasa kunne ga muryar kowa,
Ba ya karɓar horo.
Bai dogara ga Ubangiji ba,
Bai kuma kusaci Allahnsa ba.
3Shugabanninsa zakoki ne masu ruri,
Alƙalansa kuma kyarketai ne da sukan fito da maraice,
Waɗanda ba su rage kome kafin wayewar gari.
4Annabawansa sakarkari ne, maciya amana.
Firistocinsa sun ƙazantar da abin da yake mai tsarki.
Sun kuma keta dokoki.
5Ubangiji wanda yake cikinsa mai adalci ne,
Ba ya kuskure.
Yakan nuna adalcinsa kowace safiya,
Kowace safiya kuwa bai taɓa fāsawa ba.
Amma mugu bai san kunya ba.
6Ubangiji ya ce,
“Na datse al'umman duniya,
Hasumiyansu sun lalace.
Na kuma lalatar da hanyoyinsu,
Ba mai tafiya a kansu.
An mai da biranensu kufai,
Ba mutumin da yake zaune ciki.
7Na ce, hakika za ka ji tsorona,
Ka kuma karɓi horo.
Ba za a rushe wurin zamanta ba
Bisa ga hukuncin da na yi mata.
Amma suka ɗokanta su lalatar da ayyukansu.
8“Domin haka ni Ubangiji na ce,
Ku jira ni zuwa ranar da zan tashi in yi tuhuma.
Gama na ƙudura zan tattara al'umman duniya, da mulkoki,
Don in kwarara musu hasalata
Da zafin fushina,
Gama zafin kishina
Zai ƙone dukan duniya.
9“Sa'an nan zan sauye harshen mutane da harshe mai tsabta,
Domin dukansu su yi kira ga sunan Ubangiji,
Su kuma bauta masa da zuciya ɗaya.
10Gama daga hayin kogunan Habasha,
Masu yi mini sujada,
Mutanena da yake warwatse,
Za su kawo mini hadaya.
11A wannan rana ba za a kunyatar da kai ba,
Saboda tayarwar da ka yi mini ta wurin ayyukanka.
Gama a sa'an nan zan fitar da masu girmankai
Da masu fankama daga cikinka,
Ba za ka ƙara yin alfarma ba
A dutsena tsattsarka.
12Zan kuwa bar mutane masu tawali'u,
Da masu ladabi a cikinka,
Su kuwa za su nemi mafaka a wurin Ubangiji.
13 # W.Yah 14.5 Waɗanda suka ragu cikin Isra'ila,
Ba za su aikata mugunta ba,
Ba kuma za su faɗi ƙarya ba,
Gama harshen ƙarya ba zai kasance a bakinsu ba.
Za su yi kiwo, su kwanta,
Ba wanda zai tsorata su.”
Waƙar Murna
14Ki raira waƙa da ƙarfi, ya ke Sihiyona!
Ki ta da murya, ya Isra'ila!
Ki yi murna, ki yi farin ciki,
Ya ke Urushalima!
15Ubangiji ya kawar miki da hukuncinsa,
Ya kuma kori abokan gābanki.
Ubangiji Sarkin Isra'ila, yana a tsakiyarki,
Ba za ki ji tsoro ba.
16A wannan rana za a ce wa Urushalima,
“Kada ki ji tsoro, ke Sihiyona,
Kada ki bar hannuwanki su raunana.
17Ubangiji Allahnki yana tsakiyarki,
Mayaƙi mai cin nasara ne.
Zai yi murna, ya yi farin ciki da ke.
Zai sabunta ki da ƙaunarsa.
Zai kuma yi murna da ke ta wurin raira waƙa da ƙarfi.
18Zan tara waɗanda suka yi makoki domin idi,
Waɗanda suke tare da ke,
Wato waɗanda nawayar zaman talala
Ta zamar musu abin zargi.
19Ga shi kuwa, a wannan lokaci
Zan hukunta masu zaluntarki,
Zan kuma ceci gurgu,
Zan tattara korarru,
Zan mai da kunyarsu ta zama yabo,
Za su yi suna a duniya duka.
20A wannan lokaci zan komo da ku gida,
In tattara ku wuri ɗaya.
Zan sa ku yi suna,
Ku sami yabo a wurin mutanen duniya duka,
A sa'ad da na mayar muku da arzikinku,
Ni Ubangiji na faɗa.”

Currently Selected:

Zaf 3: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in

YouVersion uses cookies to personalize your experience. By using our website, you accept our use of cookies as described in our Privacy Policy