YouVersion Logo
Search Icon

Zak 6

6
Wahayin Karusai Huɗu
1Na kuma ɗaga idona, sai na ga karusa huɗu suna fitowa daga tsakanin duwatsu biyu. Duwatsun kuwa na tagulla ne. 2#W.Yah 6.4; W.Yah 6.5 Dawakai aharasai ne suke jan karusa ta fari, ta biyu kuwa akawalai ne suke janta. 3#W.Yah 6.2 Na uku kuma dawakai kiliyai ne suke janta, ta huɗu kuwa hurdu ne yake janta. 4Sa'an nan na ce wa mala'ikan da yake magana da ni, “Mene ne waɗannan, ya ubangijina?”
5 # W.Yah 7.1 Ya ce mini, “Waɗannan su ne ruhohi huɗu waɗanda suka fito daga sama bayan da sun nuna kansu a gaban Ubangijin duniya duka. 6Karusar da akawalai suke ja, za ta tafi ƙasar arewa, wadda kuma dawakai kiliyai suke ja, za ta bi su. Wadda kuwa hurde suke ja, za ta tafi ƙasar kudu.” 7Sa'ad da ingarmun suka fita, sai suka ƙagauta su zagaya duniya don su bincike ta. Ya ce musu kuwa, “Ku tafi, ku bincike duniya, kuna kai da kawowa.” Har kuwa suka yi. 8Ya kuma kira ni, ya ce, “Duba, waɗanda suka tafi ƙasar arewa sun sa fushin Ubangiji ya huce.”
Kwatancin Naɗawar Yoshuwa
9Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce, 10“Ka karɓi sadaka daga Heldai, da Tobiya, da Yedaiya waɗanda suka komo daga bautar talala a Babila. A ranar kuma ka tafi gidan Yosiya ɗan Zafaniya. 11Ka karɓi azurfa da zinariya a wurinsu, ka ƙera kambi, ka sa shi a kan Yoshuwa, ɗan Yehozadak, babban firist. 12#Irm 23.5; 33.15; Zak 3.8 Ka kuwa ce masa, ‘Ubangiji Mai Runduna ya ce, mutumin da sunansa Reshe, zai yi girma a inda yake, zai kuma gina Haikalin Ubangiji. 13Shi ne zai gina Haikalin Ubangiji, ya kuma sami girma, ya yi mulki kamar sarki, ya kuma zama firist. Kome kuwa zai tafi daidai.’ 14Kambin zai kasance a Haikalin Ubangiji don tunawa da Heldai, da Tobiya, da Yedaiya, da Yosiya ɗan Zafaniya.
15“Waɗanda yake nesa za su zo su gina Haikalin Ubangiji. Za ku kuwa sani Ubangiji Mai Runduna ya aiko ni wurinku. Wannan zai faru idan kun yi biyayya sosai da muryar Ubangiji Allahnku.”

Currently Selected:

Zak 6: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in