YouVersion Logo
Search Icon

Zak 5

5
Wahayin Littafi na Tashi Sama
1Da na ɗaga idona sama kuma, sai na ga littafi mai tashi a sama. 2Sai mala'ikan ya tambaye ni ya ce, “Me ka gani?”
Na amsa, “Na ga littafi mai tashi a sama, tsawonsa kamu ashirin ne, fāɗinsa kuma kamu goma.”
3Sa'an nan ya ce mini, “Wannan la'ana ce wadda take tashi bisa ƙasa duka. Gama za ta datse ɓarawo da mai rantsuwa da ƙarya. 4Ubangiji Mai Runduna ya ce, ‘Zan aika da littafin a gidan ɓarawo da gidan mai rantsuwa da sunana a kan ƙarya. Littafin zai zauna a gidansa, ya ƙone gidan, da katakan, da duwatsun.’ ”
Wahayin Mace a cikin Kwando
5Sa'an nan mala'ikan da yake magana da ni ya matso, ya ce mini, “Ka ɗaga idonka, ka ga abin nan da yake fitowa.”
6Ni kuwa na ce masa, “Mene ne wannan?”
Ya ce, “Wannan babban kwando ne wanda ya fita.” Ya kuma ce, “Wannan mugunta ce a dukan ƙasar.”
7Da aka ɗaga murfin kwando na darma, sai ga mace tana zaune a cikin kwandon!
8Sai ya ce, “Wannan mugunta ce.” Sa'an nan ya tura ta cikin kwandon, ya rufe bakin kwandon da murfi na darma mai nauyi. 9Da na ɗaga idona, sai na ga mata biyu suna matsowa. Iska tana hura fikafikansu, gama suna da fikafikai kamar na shamuwa. Suka ɗaga kwandon sama.
10Sai na tambayi mala'ikan da yake magana da ni, na ce, “Ina za su kai kwandon?”
11Ya ce mini, “Za su tafi da shi ƙasar Shinar don su gina masa haikali, sa'ad da suka gama ginin, za su ajiye shi a ciki.”

Currently Selected:

Zak 5: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in