W.W 7
7
1Ƙafafunki suna da kyau da takalmi,
Ke mafificiyar budurwa!
Tsarin cinyoyinki kamar aikin gwanin sassaƙa ne.
2Cibinki kamar finjali ne, wanda bai taɓa rasa gaurayayyen ruwan inabi a ciki ba.
Kwankwasonki kamar damin alkama ne a tsakiyar bi-rana.
3Mamanki kamar bareyi biyu ne, wato tagwayen barewa ne.
4Wuyanki kamar hasumiyar hauren giwa ne.
Idonki kamar tafki ne cikin birnin Heshbon,
Kusa da ƙofar Bat-rabbim.
Hancinki kyakkyawa ne kamar hasumiyar Lebanon ta tsaron Dimashƙu.
5Kin ɗaga kanki sama kamar Dutsen Karmel.
Kitsattsen gashin kanki kamar shunayya mafi kyau ne,
Yakan kama hankalin sarki.
Daɗin Soyayyar Amarya da Ango
6Ke kyakkyawa ce ƙaunatacciyata,
Kina sa ni jin daɗi a rai.
7Kina da kyan gani kamar itacen dabino,
Mamanki kamar nonnan dabino.
8Zan hau itacen dabino in tsinko 'ya'yan.
Mamanki kamar nonnan inabi suke a gare ni.
Numfashinki kamar ƙanshin gawasa ne.
9Bakinki kamar ruwan inabi mafi kyau ne.
Idan haka ne bari ya bulbulo sosai zuwa ga ƙaunataccena,
Ya gangara leɓunan masu barci.
10Ni ta ƙaunataccena ce, yana bukatata.
11Zo saurayina, bari mu tafi waje,
Mu kwana a karkara.
12Za mu tashi da sassafe, mu duba kurangun inabi,
Mu ga ko sun fara tohowa,
Ko furanni sun fara buɗewa.
Mu ga ko itatuwan rumman sun yi fure.
A can zan bayyana maka ƙaunata.
13Za ka ji ƙanshin shuke-shuke
Da na dukan 'ya'yan itatuwa masu daɗi.
Na adana maka jin daɗi na dā da na yanzu, ya ƙaunataccena.
Currently Selected:
W.W 7: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979