YouVersion Logo
Search Icon

W.W 8

8
1Da ma a ce kai ɗan'uwana ne, wanda mahaifiyata ta goya,
Da in na gamu da kai a titi,
Sai in sumbace ka, ba wanda zai kula.
2Sai in kai ka gidan mahaifiyata,
In ba ka gaurayayyen ruwan inabina wanda aka yi da rumman, ka sha.
3In ta da kai da hannun hagunka,
Ka rungume ni da hannun damanka.
4Ku yi mini alkawari, ku matan Urushalima,
Ba za ku shiga tsakaninmu ba.
Waƙa ta Shida
Ƙauna Tana da Iko kamar Mutuwa
5Wace ce take zuwa daga cikin jeji,
Kafaɗa da kafaɗa da ƙaunataccenta?
A ƙarƙashin itacen gawasa na farkar da ke,
A wurin da aka haife ki,
Wurin da mahaifiyarki ta haife ki.
6Kada ki ƙaunaci kowa sai ni,
Kada ki rungume kowa sai ni.
Ikon ƙauna kamar na mutuwa ne,
Ƙarfin kishin ƙauna kamar na mutuwa ne.
Yakan kama kamar wuta,
Yakan ci kamar gagarumar wuta.
7Kome yawan ruwa ba zai iya kashe ta ba.
Ba rigyawar da za ta nutsar da ita.
Duk wanda ya ce zai iya sayen ƙauna da dukiya,
Ba abin da zai same shi sai tashin hankali.
8Muna da 'yar'uwa ƙunƙuma.
Me za mu yi idan wani saurayi ya ce yana sonta?
9Da a ce ita bango ce, da mun gina mata hasumiyar azurfa.
Da a ce ita ƙofa ce, da mun yi mata ƙyaure da itacen al'ul.
10Ni bango ce, doguwa, mamana tantsai tantsai,
Na sami kwarjini wurin ƙaunataccena.
11Sulemanu yana da gonar inabi
A Ba'al-hamon, wato wuri mai yawan albarka.
Ya yi ijara da waɗansu zaɓaɓɓun manoma.
Kowannensu yana biyansa kuɗi, azurfa dubu.
12Ni ma ina da gonar inabi ta kaina.
Kai Sulemanu zan ba ka kuɗi azurfa dubu,
Sauran ma'aikata kuma zan ba kowanne ɗari biyu.
13Aminaina suna kasa kunne ga ƙaunataccena.
Ina so in ji muryarka daga cikin lambun.
14Ya ƙaunataccena, ka zo wurina da sauri, kamar batsiya,
Ko sagarin kishimi a kan duwatsu inda kayan yaji yake tsirowa.

Currently Selected:

W.W 8: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in