YouVersion Logo
Search Icon

W.W 6

6
1Ke mafi kyau cikin matan,
Ina ƙaunatacce naki ya tafi?
Wace hanya ƙaunatacce naki ya bi?
Za mu taimake ki nemansa.
2Ƙaunataccena ya tafi lambunsa inda fangulan furanninsa suke.
Yana kiwon garkensa a lambun, yana tattara furannin bi-rana.
3Ƙaunataccena nawa ne, ni kuma tasa ce,
Yana kiwon garkensa a cikin bi-rana.
Waƙa ta Biyar
Ango Ya Yabi Amarya
4Ƙaunatacciyata, kina kyakkyawa kamar Urushalima,
Kyakkyawa kuma kamar birnin Tirza,
Kina da shiga rai kamar ɗaya daga cikin biranen nan.
5Ki daina dubana gama idanunki suna rinjayata,
Gashinki yana zarya kamar garken awaki
Da yake gangarowa daga tuddan Gileyad.
6Haƙoranki farare fat kamar tunkiyar da aka yi mata sausaya
Aka yi mata wanka nan da nan.
Ba giɓi, suna nan shar.
An jera su tantsai.
7Kumatunki suna haske bayan lulluɓi.
8Ina da matan aure sittin, kowace kuwa sarauniya ce,
Da ƙwaraƙwarai tamanin, da 'yan mata kuwa ba a magana!
9Amma ɗaya kaɗai nake ƙauna,
Ita kyakkyawa ce kamar kurciya.
Tilo ce ga mahaifiyarta, 'yar lele ce ga mahaifiyarta.
Mata duk sukan dube ta, su yaba.
Matan sarki da ƙwaraƙwaransa suka raira waƙa suka yabe ta.
10Wace ce wannan, kamar ketowar alfijir?
Ita kyakkyawa ce mai haske, kamar hasken rana,
Ko na wata mai kashe ido.
11Na gangara zuwa cikin itatuwan almond
Domin in ga ƙananan itatuwan da suke a kwarin,
Domin in ga ganyayen inabi
Da furannin itatuwan rumman.
12Ina karkaɗuwa, don kin sa in ƙosa saboda ƙauna,
Kamar mai korar dawakan karusar yaƙi.
13Komo, ki komo, ke Bashulamiya,
Ki komo, ki komo domin mu ƙara dubanki.
Me ya sa kuke so ku dubi Bashulamiya,
Sa'ad da take taka rawar zamanin dā?

Currently Selected:

W.W 6: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in