W.W 5
5
1Na shiga cikin lambuna, budurwata, amaryata,
Ina tattara mur da ƙaro.
Ina shan zuma da kakinsa.
Ina shan ruwan inabi da madara kuma.
Ƙaunatattuna, ku ci ku sha, har ku bugu da ƙauna!
Waƙa ta Huɗu
Shan Kewa
2Ina barci, amma zuciyata na a farke,
Sai na ji ƙaunataccena yana ƙwanƙwasa ƙofa.
Buɗe mini in shigo, ƙaunatacciyata, budurwata, kurciyata,
Wadda ba wanda zai kushe ki.
Kaina ya jiƙe da raɓa,
Gashina ya yi danshi da laimar ƙāsashi.
3Na riga na tuɓe tufafina, in sāke sa su kuma?
Na wanke ƙafafuna, in sāke ɓata su?
4Ƙaunataccena ya janye hannunsa daga ƙofa,
Zuciyata kuwa tana kansa.
5Sai na tashi don in buɗe wa ƙaunataccena, ya shigo.
Hannuna sharkaf da mur,
Yatsuna suna ɗiga da mur sa'ad da na kama hannun ƙofar.
6Na buɗe wa ƙaunataccena ƙofa, amma ya riga ya tafi!
Na so in ji muryarsa ƙwarai!
Na neme shi, amma ban same shi ba.
Na yi kiransa, amma ba amsa.
7Matsara masu kai da kawowa cikin birni suka same ni,
Suka doke ni suka yi mini rauni.
Matsaran da suke kan garu suka fige gyalena.
8Ku yi mini alkawari ku matan Urushalima,
Idan kun ga ƙaunataccena,
Ku faɗa masa na yi suwu saboda ƙauna.
9Ke mafi kyau cikin mata,
Ki faɗi yadda ƙaunatacce naki yake.
Wane abin sha'awa take gare shi,
Har da za mu yi miki alkawari?
Amarya Ta Yabi Ango
10Ƙaunataccena kyakkyawa ne ƙaƙƙarfa kuma,
Da ƙyar a sami ɗaya irinsa a cikin dubu goma.
11Gashin kansa dogaye ne suna zarya,
Baƙi wulik kamar jikin shaya.
Kansa ya fi zinariya daraja.
12Idanunsa kamar na kurciyoyi a bakin ƙorama,
Waɗanda suka yi wanka da madara suna tsaye a bakin rafi.
13Kumatunsa kyawawa ne kamar lambu,
Wanda yake cike da tsire-tsire da kayan yaji.
Leɓunansa kamar furen bi-rana ne, suna bulbulo da mur.
14Hannuwansa kyawawa ne,
Saye da ƙawanen da aka yi musu ado da duwatsu masu daraja.
Ƙugu nasa sumul sumul ne kamar hauren giwa da aka manne da yakutu.
15Cinyoyinsa kamar ginshiƙan da aka yi da dutsen alabasta,
Aka kafa su a cikin kwasfar zinariya.
Kamanninsa kamar Dutsen Lebanon ne,
Da itatuwan al'ul ɗinsa mafi kyau.
16Bakinsa yana da daɗin sumbata,
Kome nasa yana faranta mini rai.
Matan Urushalima, yadda ƙaunataccena yake ke nan.
Currently Selected:
W.W 5: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979