W.Yah 8
8
Hatimi na Bakwai da Tasar Zinariya
1Sa'ad da Ɗan Ragon ya ɓamɓare hatimi na bakwai, aka yi shiru a Sama kamar na rabin sa'a. 2Sa'an nan na ga mala'ikun nan bakwai da suke a tsaye a gaban Allah, an ba su ƙaho bakwai. 3#Amos 9.1; Fit 30.1,3 Ga kuma wani mala'ika ya zo ya tsaya a gaban bagadin ƙona turare, riƙe da tasar zinariya ta turaren ƙonawa. Sai aka ba shi turare mai yawa, domin ya haɗa da addu'o'in tsarkaka duka a kan bagadin ƙona turare na zinariya a gaban kursiyin. 4Sai hayaƙin turaren ya tashi daga hannun mala'ikan tare da addu'o'in tsarkaka, ya isa a gaban Allah. 5#L.Fir 16.12; Eze 10.2; Fit 19.16; W.Yah 11.19; 16.18 Sai mala'ikan ya ɗauki tasar nan ta turaren ƙonawa, ya cika ta da wuta daga bagadin ƙona turare, ya watsa a kan duniya, sai aka yi ta aradu, da ƙararraki masu tsanani, da walƙiya, da kuma rawar ƙasa.
Ƙahonin
6Sa'an nan mala'ikun nan bakwai masu ƙaho bakwai ɗin nan, suka yi shirin busa su.
7 #
Fit 9.23-25; Eze 38.22 Mala'ikan farko ya busa ƙahonsa, sai ga ƙanƙara da wuta, gauraye da jini. Aka zuba su a duniya, sai sulusin duniya ya ƙone, sulusin itatuwa suka ƙone, dukkan ɗanyar ciyawa kuma ta ƙone.
8Mala'ika na biyu ya busa ƙahonsa, sai aka jefa wani abu a teku kamar babban dutse mai tsawo, mai cin wuta. Sulusin teku ya zama jini, 9sulusin halittar da suke a ruwa suka mutu, sulusin jiragen ruwa kuma suka hallaka.
10 #
Ish 14.12
Mala'ika na uku ya busa ƙahonsa, sai wani babban tauraro ya faɗo daga sama, yana cin wuta kamar cukwima. Ya faɗa a sulusin koguna da maɓuɓɓugan ruwa. 11#Irm 9.15 Sunan tauraron kuwa Ɗaci. Sulusin ruwa ya zama mai ɗaci, sai mutane da yawa suka mutu saboda shan ruwan, don ɗacinsa.
12 #
Ish 13.10; Eze 32.7; Yow 2.10,31; 3.15 Mala'ika na huɗu ya busa ƙahonsa, sai aka bugi sulusin rana, da sulusin wata, da kuma sulusin taurari, har sulusin haskensu ya zama duhu, wato ba haske a sulusin yini, haka kuma a sulusin dare.
13Sa'an nan da na duba, na ji wani juhurma mai jewa a tsakiyar sararin sama, yana kuka da ƙarfi, yana cewa, “Kaito! Kaito! Kaitonku, ku mazaunan duniya, in an yi busan sauran ƙahonin da mala'ikun nan uku suke shirin busawa!”
Currently Selected:
W.Yah 8: HAU
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979