YouVersion Logo
Search Icon

W.Yah 7

7
Adadin Waɗanda aka Buga wa Hatimin, 144,400 na Isra'ila
1 # Irm 49.36; Dan 7.2; Zak 6.5 Bayan wannan na ga mala'iku huɗu, a tsaye a kusurwa huɗu ta duniya, suna tsare da iskokin nan huɗu na duniya, don kada wata iska ta busa a kan ƙasa, ko a kan teku, ko a kan wani itace. 2Sai na ga wani mala'ika yana hawa daga mafitar rana, riƙe da hatimin Allah Rayayye. Sai ya yi wa mala'ikun nan huɗu magana da murya mai ƙarfi, waɗanda aka bai wa ikon azabtar da ƙasa da teku, 3#Eze 9.4,6 yana cewa, “Kada ku azabtar da ƙasa, ko teku, ko itatuwa, sai mun buga wa bayin Allahnmu hatimi a goshinsu tukuna.” 4Sai na ji adadin waɗanda aka buga wa hatimin, dubu ɗari da arba'in da huɗu ne, daga kowace kabilar Isra'ila, 5wato, an yi wa dubu goma sha biyu hatimi daga kabilar Yahuza, dubu goma sha biyu daga kabilar Ra'ubainu, dubu goma sha biyu daga kabilar Gad, 6dubu goma sha biyu daga kabilar Ashiru, dubu goma sha biyu daga kabilar Naftali, dubu goma sha biyu daga kabilar Manassa, 7dubu goma sha biyu daga kabilar Saminu, dubu goma sha biyu daga kabilar Lawi, dubu goma sha biyu daga kabilar Issaka, 8dubu goma sha biyu daga kabilar Zabaluna, dubu goma sha biyu daga kabilar Yusufu, dubu goma sha biyu kuma daga kabilar Biliyaminu.
Ƙasaitaccen Taro daga Kowace Al'umma
9Bayan wannan na duba, ga wani ƙasaitaccen taro, wanda ya fi gaban ƙirge, daga kowace al'umma, da kabila, da jama'a, da harshe, suna a tsaitsaye a gaban kursiyin, a gaban Ɗan Ragon kuma, a saye da fararen riguna, da gazarin dabino a hannunsu, 10suna ta da murya da ƙarfi suna cewa, “Yin ceto ya tabbata ga Allahnmu wanda yake a zaune a kan kursiyin, da kuma Ɗan Rago!” 11Dukan mala'iku kuwa suna tsaitsaye a kewaye da kursiyin, da dattawan nan, da kuma rayayyun halittan nan guda huɗu, suka fāɗi a gaban kursiyin suka yi wa Allah sujada, 12suna cewa, “Hakika! Yabo, da ɗaukaka, da hikima, da godiya, da girma, da iko, da ƙarfi su tabbata ga Allahnmu har abada abadin! Amin! Amin!”
13Sai ɗaya daga cikin dattawan nan ya yi mini magana, ya ce, “Su wane ne waɗannan da suke a saye da fararen riguna, daga ina kuma suke?” 14#Dan 12.1; Mat 24.21; Mar 13.19 Sai na ce masa, “Ya shugaba, ai, ka sani.” Sai ya ce mini, “Su ne waɗanda suka fito daga matsananciyar wahala, sun wanke rigunansu, suka mai da su farare da jinin Ɗan Ragon nan. 15Saboda haka ne suke a gaban kursiyin Allah, suna bauta masa dare da rana a Haikalinsa. Na zaune a kan kursiyin nan kuwa, zai kare su da Zatinsa, 16#Ish 49.10 ba za su ƙara jin yunwa ba, ba kuma za su ƙara jin ƙishirwa ba, ba za su ƙara jin zafin rana ko ƙuna ba sam, 17#Zab 23.1; Eze 34.23; Zab 23.2; Ish 49.10; Ish 25.8 domin Ɗan Ragon nan da yake a tsakiyar kursiyin, shi zai zama makiyayinsu, zai kuwa kai su maɓuɓɓugar ruwan rai. Allah kuma zai share musu dukan hawaye.”

Currently Selected:

W.Yah 7: HAU

Highlight

Copy

Compare

Share

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in