1
W.Yah 8:1
Littafi Mai Tsarki
HAU
Sa'ad da Ɗan Ragon ya ɓamɓare hatimi na bakwai, aka yi shiru a Sama kamar na rabin sa'a.
Compare
Explore W.Yah 8:1
2
W.Yah 8:7
Mala'ikan farko ya busa ƙahonsa, sai ga ƙanƙara da wuta, gauraye da jini. Aka zuba su a duniya, sai sulusin duniya ya ƙone, sulusin itatuwa suka ƙone, dukkan ɗanyar ciyawa kuma ta ƙone.
Explore W.Yah 8:7
3
W.Yah 8:13
Sa'an nan da na duba, na ji wani juhurma mai jewa a tsakiyar sararin sama, yana kuka da ƙarfi, yana cewa, “Kaito! Kaito! Kaitonku, ku mazaunan duniya, in an yi busan sauran ƙahonin da mala'ikun nan uku suke shirin busawa!”
Explore W.Yah 8:13
4
W.Yah 8:8
Mala'ika na biyu ya busa ƙahonsa, sai aka jefa wani abu a teku kamar babban dutse mai tsawo, mai cin wuta. Sulusin teku ya zama jini
Explore W.Yah 8:8
5
W.Yah 8:10-11
Mala'ika na uku ya busa ƙahonsa, sai wani babban tauraro ya faɗo daga sama, yana cin wuta kamar cukwima. Ya faɗa a sulusin koguna da maɓuɓɓugan ruwa. Sunan tauraron kuwa Ɗaci. Sulusin ruwa ya zama mai ɗaci, sai mutane da yawa suka mutu saboda shan ruwan, don ɗacinsa.
Explore W.Yah 8:10-11
6
W.Yah 8:12
Mala'ika na huɗu ya busa ƙahonsa, sai aka bugi sulusin rana, da sulusin wata, da kuma sulusin taurari, har sulusin haskensu ya zama duhu, wato ba haske a sulusin yini, haka kuma a sulusin dare.
Explore W.Yah 8:12