1
W.Yah 7:9
Littafi Mai Tsarki
HAU
Bayan wannan na duba, ga wani ƙasaitaccen taro, wanda ya fi gaban ƙirge, daga kowace al'umma, da kabila, da jama'a, da harshe, suna a tsaitsaye a gaban kursiyin, a gaban Ɗan Ragon kuma, a saye da fararen riguna, da gazarin dabino a hannunsu
Compare
Explore W.Yah 7:9
2
W.Yah 7:10
suna ta da murya da ƙarfi suna cewa, “Yin ceto ya tabbata ga Allahnmu wanda yake a zaune a kan kursiyin, da kuma Ɗan Rago!”
Explore W.Yah 7:10
3
W.Yah 7:17
domin Ɗan Ragon nan da yake a tsakiyar kursiyin, shi zai zama makiyayinsu, zai kuwa kai su maɓuɓɓugar ruwan rai. Allah kuma zai share musu dukan hawaye.”
Explore W.Yah 7:17
4
W.Yah 7:15-16
Saboda haka ne suke a gaban kursiyin Allah, suna bauta masa dare da rana a Haikalinsa. Na zaune a kan kursiyin nan kuwa, zai kare su da Zatinsa, ba za su ƙara jin yunwa ba, ba kuma za su ƙara jin ƙishirwa ba, ba za su ƙara jin zafin rana ko ƙuna ba sam
Explore W.Yah 7:15-16
5
W.Yah 7:3-4
yana cewa, “Kada ku azabtar da ƙasa, ko teku, ko itatuwa, sai mun buga wa bayin Allahnmu hatimi a goshinsu tukuna.” Sai na ji adadin waɗanda aka buga wa hatimin, dubu ɗari da arba'in da huɗu ne, daga kowace kabilar Isra'ila
Explore W.Yah 7:3-4